✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin tsaron kasarmu ya ruguje-Majalisa

Majalisar Dattawan Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda harkokin tsaro ya tabarbare a kasa baki daya tare da rushewar tsarin tsaron kasar baki daya. ’Yan…


Majalisar Dattawan Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda harkokin tsaro ya tabarbare a kasa baki daya tare da rushewar tsarin tsaron kasar baki daya.
’Yan majalisar sun yi furucin ne yayin da suke tafka muhawara kan kisan da ’yan bindiga suka yi wa mutane a karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara.
Kudurin wanda Sanata Tijjani Kaura dan jam’iyyar APC daga jihar Zamfara ya dauki nauyi wanda Sanata Ahmed Sani Yerima dan jam’iyyar APC ya goyawa baya.