✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsarin Rabon Naman Ragon Layyan Sarkin Kano

Yadda ake samowa da shirya ragon Layyan Sarkin Kano da kuma yadda ake rabon naman

Daraktan Sashen Bincike da Fasahar Sadarwa na Kotun Daukaka Kara ta Shari’ar Musulinci, kuma mai bincike kan harkokin Al’adu, Malam Nasir Wada Khali, ya bayyana cewa rashin sanin harkar gudanarwar masarautun gargajiya ne ya sa mutane ke tunanin ba a bibiyar ganin watan Musulunci sai na azumi da Karamar Sallah kawai.

Ya bayyana hakan ne ta cikin wani shiri da wani gidan rediyo mai zaman kansa a Kano ke gabatarwa.

Khalil ya ce rashin sani da bincike ne ya sanya ba su san cewa a duk karshen wata da dare ana zama a wata fada da ke bangaren Arewa a gidan Sarki ba.

Ya ce bangaren shi ne ya ce tafi kowanne dadewa kuma a nan ake sanar da ganin wata, tun ma kafin dawowar Masarautar Kano karkashin Daular Sakkwato.

Ganin wata Azumi da Sallah

Ya ce “Ba wai watan Azumi ko na Karamar Sallah ba ne kadai ake dubowa, sauran watannin ana gani ne a matakin karamar hukuma, sai hakimi ya rubuto wa Masarauta cewa an ga wata a guri kaza.

“Amma watanni uku  ba da rahotanni ake amfani ba, gaban sarki ake zuwa a fada — wato watannin Azumi da Sallah Karama da Babba.

“Amma ba a Kofar Kudu inda fadoji bakwai suke ba, a bangaren Kofar Arewa ne.

“Watakila don  an saba idan aka ga watan Karamar Sallah ana kwana kade-kade ne su kuma a sauran ba a yi, musamman na Babbar Sallah da har sai an je tara ga wata, wato jajibiri sannan ake wadancan kade-kaden.

Jajibirin Sallah

“Dalilin hakan kuwa shi ne kasancewar ana jajibirin azumi, akwai batun tashi da azumin farilla, a sauran kuma babu,” in ji shi.

Sai dai ya ce ranar jajibirin Babbar Sallar kamar ta Karamar Sallah, ana kiran daren da ‘Waza’.

Ya bayyana cewa a ranar kwana ake ana kade-kaden sarauta da ba na yau da kullum ba, irisu kaho da kuge da algaita da tambari da sauransu.

Sai kuma harba bindigogin gargajiya a iska da shi ma ake kwana ana yi domin tuna wa mutane cewa washegari Sallah.

Ranar Sallar Idi

Ya ci gaba da cewa, “Idan kuma gari ya waye, ranar Sallah ke nan, ko Babba ko Karama, Sarki zai yi ado da sabbin kaya farare, kamar dai na ranar Juma’a, don koyi da abin da Annabi (SAW) ya ce, wato yin ado da sabon kaya ranar sallah, ranar Juma’a kuma fari, to sai sarki sai ya hada biyun”.

Amma ya ce a yanzu sarakunan kan sa tufafi ruwan madara a madadin fari da aka saba gani, amma su ma sabbi ne.

Yankan ragon Sarki

Sannan a wannan hawa na Idi ba a kirari sai dai karatun Dala’ilu da Ishiriniya, domin tunatar da shi Allah, har ya je ya dawo.

“Bayan Sallar Idi, a Babbar Sallah sarki zai yanka ragon da ake kira Alhajin Rago ko kuma Mai Alwala.

“To daga nan kowa kuma a gari sai ya koma gida ya yanka nasa, daga nan a ci gaba da sauran shagulgulan Sallah,” in ji shi.

Nau’ikan ragunan da sarki ke yankawa

Ya ci gaba da cewa: “Ragon cikin gida shi ne Alhajin Rago, kuma fari tas yake.

“Saboda ragunan kala-kala ne, ya danganta da kasar da aka kawo su da kuma launinsu.

“Akwai Balamin Rago na yankin Chadi, shi za ka gan shi da doro da malolo.

“Sai wanda ake kira Uda, marar fada ke nan; dogo ne da bai da maiko, na yankin Nijar,” in ji Wada Khalil.

Samowa da shirya ragon Sarki

Malam Nasir ya ci gaba da cewa wadanda alhakin samo Ragon Layyar Sarki ke kansu su ne Yaran Sarkin Hatsi, wanda ke kula da harkar addini na gidan sarkin baki daya.

Ya ce da zarar an samu ragon, wanke shi ake yi a daren jajibirin ko kuma da safe.

Gidan Sarkin Hatsin a Kofar Kudu yake a gidan sarkin, inda ake gabatar da Sallar Idi kuma yana Kofar Mata da ke Arewa maso Gabashin gidan kuma ta nan ne ake shigo da ragon, inda Sarki zai gani ya shafa shi kafin ya fita idin.

“Idan ya shafa shi zai masa addu’a ya ce ‘Allahuma rabbana takabbal minna wa barik lana’.

Yanka ragon Layyan Sarki

“Ragon na riga sarki zuwa masallacin Juma`a, daga nan kuma zai wuce sallah, idan an idar kuma a yanka shi.

“Sai duka al`ummar gari su ma su yanka, amma ban san ko har yaznu haka ake ba.

“Duk wanda dai sarki ya ce ya yanka shi yake yankawa ko liman ko Waziri, ya dai kasance malami ne wanda ya san shar’iar yankan”, in ji shi.

Tabarmar ragon Sarki

“Dama tun ana jajibirin Babbar Sallah za a samo karauni guda hudu, wato tabarma ke nan.

“Daya ta sarki ce da zai yi Sallar Idi a kai, daya ta Gwamna, daya ta Liman, sai daya ta ragon da za a yanka na sarki a dora ce.

“Amma da karamar sallah uku ake kawowa, sai dai ban da masaniyar ko har yanzu haka ake yi.”

Ya bayyana cewa bayan an yanka ragon, bawan sarki ke daukar shi ya kai fada inda za a yi fida a kuma sarrafa.

Da bawan ya je sai ya sauke shi a soron Jakadiya inda ake aikin rago kuma akan ’yanta duk bawan da ya kai ragon da aka yanka fada.

Daga nan sai a cire hanta, kamar dai yadda addini ya tsara rike bakin ranar sallah da karyawa da hantar abin Layya.

Malam Nasir ya ce a da dai Uwar Soro ce ke aikin, amma a yanzu ba shi da tabbas kan yadda tsarin yake.

Rabon naman ragon Layya

Ya ce duk wani babban hakimi da ’yan majalisar sarki da kuma wanda ke cikin gida da bayi har ma da iyalansa da duk wanda ya wuce ya ga lokacin da ake sarrafwa ko ake rabon naman sallan da su ake rabon naman.

Sai dai ya ce fatar kuma ya manta yadda ake da ita, amma ya ce ya san ana buzu da ita.

Al’adar kawo wa Sarki ragon Layya

“Sarkin Kano Sulaimanu, akwai shekarar da ta zo ba shi da ragon da zai yi Layya da shi saboda ba hali, sakamakon shugabancin da ba irin na yanzu ba ne.

“Sai hakimai ne suka kawo masa da shekara ta zagayo, to daga nan ne sai ya zamo al’ada hakimai za su kawo wa sarki rago duk Sallah Babba, gwargwadon wadatarka, don gudun aukuwar wancan lamari na baya.

“To a cikin wadannan ake hadowa da Alhajin Rago ko Mai alwala; amma dai sarki shi ke sayen ragonsa da kudinsa yanzu, ba a wadancan yake dauka ba.

“Su wadannan ana raba su ne ga mutane da dama da iyalai da mutanen gida, ya dai danganta da wadatar yadda aka samu.