Wani jami’in kiwon lafiya a Jihar Maharashtra da ke kasar Indiya ya ce, an samu rahoton rasuwar mutane da ake kyautata zaton na da alaka da sankarau a wasu yankunan karkara.
Jihar Maharashtra da ke Yammacin Indiya ta yi rajistar mutuwar mutum 25 sakamakon kamuwa da cutar sankarau sanadiyyar tsananin zafi tun daga karshen Maris, adadin da ya fi yawa a shekara biyar da suka gabata, tare da yiwuwar samun karin asarar rayuka a wani wuri a cikin kasar da ke fama da zafi sama da digiri 40 na ma’aunin Celsius.
Masana kimiyya sun danganta farkon lokacin rani mai tsanani da sauyin yanayi, kuma sun ce fiye da mutum biliyan daya a Indiya da makwabciyarta Pakistan sun kasance cikin mawuyacin hali sanadiyyar tsananin zafin.
Da sanyin damina a wata mai zuwa ake tunanin samun sauki, ga kuma yawaitar katsewar wutar lantarki a wasu sassan Indiya, hatta gidaje da ke da na’urar sanyaya daki, za su iya samun jinkiri a makonni masu zuwa.
Yawancin mutuwar a Maharashtra ta faru ne a yankunan karkara na jihar da take mafi arziki a Indiya.
Pradeep Awate, wani jami’in kiwon lafiya na Maharashtra, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa, “Wadanda ake zaton, sun rasu ne sakamakon zafin rana.”
Indiya ita ce, kasa ta biyu a yawan masu samar da alkama a duniya, amma yanayin zafi a bana ya yi tsanani, bayan shekara biyar a jere da aka samu yin noman alkama.
Yayin da wutar lantarki ke kara tabarbarewa, kamfanonin da ke samar da wutar lantarki na fama da karancin kwal kuma gwamnati na rokon su kara kaimi. Indiya ta hadu da zafi mafi tsanani a cikin watan Maris a sama da karni daya,tare da matsakaicin zafin jiki a duk fadin kasar da ya haura digiri 33.1 na ma’aunin celcius da kusan digiri 1.86 sama da na matsaikacin yanayi, a cewar Sashen Kula da Yanayi na Indiya.
Yawancin sassan Arewacin Indiya da Yamma da Gabas sun hadu da yanayin zafin da ya wuce digiri 40 na ma’aunin Celsius a watan jiya.
A Jihar Odisha da ke Gabashin kasar, hukumomi sun ce wani mutum mai shekara 64 ya mutu sakamakon cutar sankarau a ranar 25 ga Afrilu kuma ana yi wa daruruwan mutane jinya.
A Subarnapur da ke Gundumar Odisha wacce take zafi mafi muni, an samu tsananin zafin da ya kai digiri 43.2 a ma’aunin Celsius a ranar Talata.
Wani mazaunin Subarnapur, Mohana Mahakur, ya ce, “Yanayin da zafi sosai,” fanka da na’urar sanyaya daki – babu abin da suke iya yi.