Manoman rani a Jihar Taraba sun koka kan matsalar tsadar man fetur da rashin tsaro da suka ce na barazana ga sana’arsu.
Wasu daga cikin manoman da wakilin Aminiya ya zanta dasu sun ce tsadar man fetur ya taka masu birki kan burinsu na gudanar da noman mai yawa.
- NAFDAC ta kwace jabun magunguna na N20m a kasuwar Zariya
- Kotu ta yi watsi da karar aka shigar da Tinubu kan amfani da takardun bogi
Daya daga cikin manoman mai suna Alhaji Adamu Kabir ya bayyana cewa yana daya daga cikin wadanda suka yi asara a daminar da ta wuce a sanadiyya ambaliyar ruwa.
Sai dai ya ce duk da haka, ya daura niyyar yin noman shinkafa mai yawa da rani, amma dole ne ya rage burinsa a dalilin tsadar man fetur.
Ya ce a ranin bara, sun sayi litar man fetur a kan Naira 200, amma yanzu farashin ya zarce N370.
Alhaji Adamu ya kuma ce bayan tsadar man fetur akwai babban matsala ta masu sace mutane wanda ya sa manoma da yawa suka kaurace wa gonakinsu a wasu Kananan Hukumomin Jihar.
Shi ma Shugaban Kungiyar Manoman Shikafa ta kasa reshen Jihar, Alhaji Tanko Bobbi Andami ya nuna damuwa gangane da tsadar man fetur da ta tsaro wanda ya ce za su rage yawan shinkafa da masarar da za a noma a wannan ranin, in ba a dauki matakin shawo kan matsalolin ba.