An ci gaba da samun hauhawa na farashin kayayyaki a Najeriya kamar yadda Hukumar Kididdiga ta kasar ta bayyana a ranar Litinin.
Rahoton na hukumar NBS ya ce an samu hauhauwar farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi da ya kai kashi 16.82 cikin dari a watan Afrilu da ya wuce.
- Kamfanonin Jiragen Sama za su fara soke tafiye-tafiye saboda wahalar mai
- Mutum miliyan 10 yunwa za ta addaba a Yammacin Afirka
An samu hauhawar farashin kayayyakin a watanni uku a jere a bana kadai.
Alkaluman NBS sun nuna tsadar kayayyakin ta ci gaba da lunkawa a Najeriya tun 2016 kawo yanzu.
Tsadar man dizel da mafi yawanci ƴan Najeriya ke dogaro da shi wurin kasuwanci ya kara haifar da tsadar kayayyakin da kuma tasirin rikicin Ukraine.