Rahotanni daga Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON sun tabbatar da cewa har yanzu hukumar ta gaza samun kudaden da za ta biya wa mahajjatan bana dakuna da sauran abubuwan bukata a kasar Saudiyya yayin aikin Hajjin bana.
Rashin samun wadatattun kudade domin wannan aiki ya kawo cikas ga shirye-shiryen tafiya aikin Hajjin maniyyatan Najeriya.
Ranar 3 ga watan Janairu 2024 ne NAHCON ta bayyana cewa Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta sanya ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin ranar karshe domin kammala shirye-shirye da amincewa kan yadda aikin Hajji zai kasance.
- Yadda rashin lantarki da tsadar fetur ke kassara masana’antu
- ‘Kalaman Buhari Na Yabon Gwamnatin Tinubu Ba Su Dace Ba’
Kuma a wannan rana ce aka kawo karshen biyan kudade a asusun ajiyar banki na kasa da kasa (IBAN).
Aminiya ta ruwaito cewa, a yayin da hukumar NAHCON ke kokarin kammala shirye-shiryen aikin Hajjin, an samu cikas a wurin biyan kudin abinci da masauki da sufuri a lokacin aikin Hajji sakamakon rashin wadatattun kudade a hannun hukumar aikin Hajji ta Najeriya.
Ana ganin faduwar darajar Naira ne babban dalilin da ya sa har yanzu hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta gaza kammala shirye-shiryenta.
A halin da ake ciki dai kasar Saudiyya ta fara bayar da biza ga wadansu kasashen da ke niyyar tafiya aikin bana.
Mun gano cewa rashin tabbas kan ko Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai amince da ya bayar da tallafin dala ga hukumar aikin Hajjin kasar nan ya sa ake fargabar yiwuwar kara wa maniyyata kudin tafiya sauke farali a bana.
A watan Fabrairu ne NAHCON ta kayyade Naira miliyan 4.8 a matsayin kudin aikin Hajjin na shekarar 2024, inda ta ce an amince da hakan ne bayan ta karya farashin wasu hidimomin da za a yi wa maniyyata a yayin aikin Hajjin.
A lokacin da aka bayyana hakan, farashin dala na N1,410 a kasuwar bayan fage, yayin da take N1,368 a hukumance.
Mafi karancin kudin da za a biya a matsayin kudin tafiya zai kasance Naira miliyan 8.46 ko kuma Naira miliyan 8.2, wanda ya kai dala 6,000 da ake kayyade cewa za a kashewa kowane mahajjaci.
Shugaban hukumar, Jalal Ahmad Arabi, ya ce kudin zai kai “kusan Naira miliyan 6” idan ba don rangwamen da masu kwangilar hidimtawa alhazai suka yi wa Najeriya ba.
Ko da yake, Jalal bai bayyana ko nawa ne kowane mahajjaci zai biya dala ba bayan an yi rangwame.
Farashin dala ya yi tashin gwauron zabi wata daya bayan wannan sanarwar, abin da ya jefa hukumar cikin mawuyacin hali.
Hakan ta sa dole hukumar ta nemi taimakon shugaban kasa don kar a sake karawa maniyyata abin da za su biya domin halartar aikin Hajjin bana.
Kafin yanzu dai Gwamnatin Tarayya ta sha tallafa wa maniyyata da dala, wanda hakan ya sa ake samun saukin kudin tafiya.
Amma tun da aka samu matsala kan farashin kudaden kasashen ketare musamman dala, babu tabbas kan ko gwamnatin za ta iya ba da tallafin a bana.
Yayin da ake fatan gwamnati za ta shiga tsakani ta hanyar ba da tallafin wurin ba da dala a farashi mai rahusa ga hukumar aikin hajji kasar nan, an tseguntawa wa Aminiya cewa babu kyakkyawar fahimta tsakanin fadar shugaban kasa da hukumar alhazan Najeriya NAHCON.
Wannan dalilin ne ya sa NAHCON ta kasa fara biyan hukumomin aikin Hajjin da ke ƙasar Saudiyya da kuma kamfanonin da ke hidima da alhazai makonni biyu da Saudiyya ta fara bayar da biza ga maniyyatan waɗansu kasashe.
Majiyar da ta zanta da Aminiya kuma ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce hukumar na cikin rudani kan yadda za a tafiyar da aikin Hajjin na bana.
Ta ce, “Tunda hukumar ta sanar da kudin aikin Hajjin bana muke jiran Shugaban Kasa ya yanke shawara kan batun tallafin dala amma shiru.
“Rashin ba da tallafin zai janyo babbar matsala ga maniyyata, domin tabbas hakan zai shafi farashin da aka sanar har kuma maniyyata a Najeriya suka bibbiya.
“Ina kyautata zaton cewa gwamnati na yin taka-tsan-tsan saboda cin hanci da rashawa da ya biyo bayan amincewar biyan kamfanonin jiragen sama dala biliyan 24 don ayyukan da suka yi a aikin Hajjin 2023.”
Majiyar ta kuma bayyana cewa wasu sassan kasar nan sun bayyana rashin gamsuwa kan tallafin ba da dala ga Hukumar Alhazan Najeriya, kan hakan ne ake tunanin shugaban kasa ya dakatar da biyan kudaden, kuma har yanzu ba a biya kamfanonin jiragen saman da suka yi aikin jigilar Alhazan Najeriya a 2023 ba.
Majiyar ta ce, ya kamata a ce wakilan NAHCON su kasance a kasar Saudiyya a mako na biyu na watan Ramadan, domin ci gaba da shirye-shirye.
Wata majiya a daga cikin hukumomin jin dadin alhazai na jihohin kasar nan ta shaida mana cewa: “Halin da suke ciki a yanzu shi ne, babu wata ƙwaƙƙwarar magana daga fadar shugaban kasa zuwa ga shugaban NAHCON.
“Har yanzu ana ganin kamar fadar shugaban kasa ba ta da niyyar ba da tallafin da gwamnati ta saba yi, ina ganin har yanzu ba su yanke hukunci kan ko za su bayar ko ba za su bayar ba, wannan shi ne ne tushen jinkirin da aka samu.”
Ta kara da cewa, bayyanar takardar da ta tabbatar da cewa gwamnati na ba da tallafi ga hukumar ta janyo shugaban kasa ya janye duk wani tallafi ga hukumar, sannan kowa na tsoron saka baki domin abin yana neman ya dauki wani abu mai kama da kabilancin addini.
Har yanzu ana karbar kudin aikin Hajji a jihohi
Majiyar ta kuma ce har yanzu wasu hukumomin jin dadin alhazai na jihohi a kasar nan, na ci gaba da karbar kudade daga maniyyata.
Ta kuma ce wannan ne dalilin da hukumar NAHCON ta kasa sanin hakikanin adadin ‘yan Najeriya da ake sa ran za su tafi kasar Saudiyya domin sauke farali.
Abin da maniyyata ke cewa
Wadansu maniyyata da muka zanta da su sun bayyana cewa ba za su yarda su kara ko kwabo ba.
Ibrahim Haruna Shu’aibu, wani maniyyaci daga Jihar Filato ya ce, watanni biyu da suka gabata ya kammala biyan Naira miliyan 4.6, amma bai kara samun wani labari daga hukumar alhazai ba tun daga lokacin.
“Ya zuwa yanzu, na yi tsammanin za a rage farashin kudin ne biyo bayan umarnin da Shugaba Tinubu ya ba Hukumar Hajji. Na dade ina jiran jin ta bakin hukumar, amma babu wata sanarwa daga hukumar game da shirin.
“An kuma gaya mana cewa gwamnonin jihohi za su tallafa mana da dala, amma har yanzu hukumar alhazai ta Jihar Filato ba ta sanar da mu hakan ba. Babu wanda ke magana da mu,” inji Ibrahim Haruna.
Wani maniyyaci mai suna Auwal Kasimu ya bayyana damuwarsa kan yadda hukumar alhazai ta kasa da ta jiha suka bar su cikin duhu.
“An bar mu a cikin duhu, domin tun da muka biya kudin tafiya aikin Hajji, babu wani bayani da ya zo mana daga hukumar.
“Labari ne mai dadi cewa gwamnati na shirin rage kudin, amma har yanzu ba mu samu labarin ko hakan zai tabbata ba.
“Ba na son jin labarin wani kari. Idan ba su rage ba, me zai sa su ce mu ƙara, tun da mun biya watanni da suka wuce? Amma idan aka yi kari, mutum zai dubi aljihunsa ne kawai ya ga ko zai iya karawa ko a’a.”
NAHCON ta fara gunguni
Da muka tuntubi mataimakiyar daraktar hukumar NAHCON kan harkokin jama’a, Fatima Sanda, ta ce hukumar ba ta da wani karin haske da za ta yi game da lamarin.
Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Lahadi, 11 ga Fabrairun 2024, Shugaba Tinubu ya yi alkawarin tallafa wa alhazai.
Ya yi wannan alkawari ne a jawabin da ya yi yayin da tawagar kungiyar Tijjaniyya ta Duniya karkashin jagorancin Khalifa Muhammad Mahe Niass ta ziyarce shi a fadarsa da ke Abuja.
Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta dubi tsare-tsaren aikin Hajji domin samarwa alhazai tallafi domin taimakon su lokacin ibadar.
A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar fitar, ta ambato Tinubu yana jaddada muhimmancin ayyukan ibada wajen gina kasa, tare da jaddada kudirin gwamnatinsa na tallafa wa ayyukan addini.
Kungiyar ta bayyana bukatar yin hadin gwiwa tsakanin shugabannin siyasa da na addini don ciyar da muradun kasa da inganta hadin kai a tsakanin jama’a.
Wani Malamin addinin Musulunci Dokta Maisuna M. Yahya, wanda ya kafa kungiyar Al-Mustofiyyah Society of Nigeria, ya shaida wa Aminiya cewa aikin hajji ya wajaba a kan kowane Musulmi, muddin mutum yana da hanyoyin samu da suka dace da shari’a.
Ya ce ba laifi gwamnati ta sa baki wajen bayar da tallafin kudin aikin Hajjin na shekarar 2024, amma ba shi ne abin da ya fi mutane suka fi bukata ba.
“Ba laifi ba ne gwamnati ta tallafa wa aikin Hajji, amma abu na farko da ya kamata gwamnati ta fara dubawa shi ne mutane suna cikin halin kunci saboda yunwa.
“Don haka abinci ya zo na farko kafin batun tallafin aikin hajji yazo na biyu.”