✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsadar abinci: Mutanen Kebbi sun koma cin rogo

Mazauna garin Birnin Kebbi sun koma neman sauki a wurin masu dafaffen rogo.

A yanzu masu sana’ar sayar da dafaffen rogo na samun ciniki sosai a Birnin Kebbi a yayin da jama’a da dama suka koma cin rogon sakamakon hauhawar farsahin abinci da ake fama da ita.

Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa galibin gidajen sayar da gidan abinci ko dai sun kara kudi ko kuma sun rage yawan abincin da suke sayar wa kwastomominsu.

Wannan ta sanya yawancin mutane komawa cin dafaffen dogo a zaman abincinsu musamman ma ga wadanda ba sa iya zuwa gidajen abincin.

A yanzu ana ganin dumbin ’yan mata na tallar dafaffen rogon a kan titunan garin Birnin Kebbi inda matasa da tsofaffi kowa ke saya.

Wani mai suna Mamman Sale, ya ce a da yana cin abinci akalla sau uku a rana, amma yanzu saboda tsadar rayuwa ba ya iya samun hakan.

Mutumin wanda magini ne, ya ce yanzu dakyar yake samun aikin ginin, shi sa ya koma cin abinci mai araha, don haka yake cin dafaffen rogo.

“Sakamakon tsadar kayayyakin gini, samun aiki a wajenmu yanzu ya zama da wahala sosai.

“Duk da ni gwauro ne amma da kyar nake samun abinci saboda tsadarsa,” inji shi.

Ya kara da cewa abincin da a da mutum zai samu a N100 zuwa N150 yanzu ya koma N200 zuwa N250.

A cewarsa, yanzu ya fahimci dafaffen rogon shi ne mafita a gareshi saboda ba sai ya kashe kudi masu yawa zai ci ya koshi.

Wata yarinya mai sayar da dafaffen rogon ta shaida wa Aminiya cewa tana samun kasuwa sosai a kwanakin nan.

Ta ce a kwastomomin nata babu babba ko yaro, kowa na zuwa sayan dafaffen rogon.

“Ina samun ribar tsakanin N400 zuwa N500 a kullum; Ina sarin rogon N1000 a kullum. Abin ban sha’awa a kasuwancin shi ne muna samun kwastomomi da yawa gaskiya.”

%d bloggers like this: