Tsige tsittsigen tsandauri
Tsabagen tsagwaron tsauri
Tsitakar tsantsame tsiyataku tsiri-tsiri
Tsokacin tsara tsibiri
Tsaikon tsagaita tsatsubar tsumburburi
Baban aiki
A rankaya da mutan kirki
Talaka ya fice daga akurki
Gayauna a barbade ta da taki
Mai-duka ya maida koko masaki
A samar da daman hatsi
Ko ludayi ya dubi hantsi
An fice daga matsi
Ai ta motsi
Ba mai tsuwwa tsi-tsi
Shirin shiga sharo
Sai dai shanu sun hauro
Makiyayi Fullo a dauro
Kiwo kwararo-kwararo
A daina gararambar gwauro
Dubi batun su Jauro
A kira su su hallaro
A ba su horo
A gargadi bararo
A zare na-mujiya zaro-zaro
A dai kirayi taro
Bukatun kowa a tattaro
Al’umma ta gangaro
Gayyatar na-gayyaro
A’a a dai ba da goriyar goro
Adon-gari an jero
An daura awarwaro
Har da kada bambaro
’Yan lalle an tunkaro
Ai wa kasa kurin kwarkwaro
Mirgine-mirginen watan Marisa
Mamular goro marsa
Masalahar mutsuttsuke masa
Masu fuka-fuki an tasa
Mutane kar a kasa
An dai yi kissa
Kisisina ma an assasa
Har aka rasa wurin dosa
Dubi al’amura an cuccusa
Camamar ca’ammas aka kunsa
Zabuka na ta zababbaka
Zabi-ka-tika
Mai jan linzami ga mota a tuka
Nagargaru sai a mika
In an zo matsa burki za a taka
Wasu na gunguni
Da guna-guni
A duba karkara da birni
A nemi shawarar masani
Don kawo karshen rashin sani
Hasken Haurobiya
Shi ne za a bibiya
A daina duk wata kwaramniya
Lallai a cimma matsaya
A nemi ilmu a wataya
’Yan makaranta
Kyawawan ta’adu ku tallata
Rayuwar al’umma a saisaita
Kar a jefa mu kuntata
Ai ta saurutu ratata
Haurobiyawa na ta ce-ce-ku-ce kan TSOKACIN TSIRON TSARIN TSIBIRIN TSAGAITA TSATSUBAR TSUMBURBURIN TSIGE TSITTSIGEN TSANDAURI da Baban-burin-huriyya ya bijiro da shi lokacin da ya lashe zaben shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa. An baje wannan tsokaci tare da tsokale-tsokalen tsokana, haka kuma su ma masu burin ganin an tsaurara tsaro, an bai wa jami’an tsaro horo, ta yadda za su farmaki miyagun boye su gangaro. Farfajiyar koyon watsattsake da bude wagagen littattafai ’yan dugwi-dugwi su hallaro don su yaki juhala, su samu masalahar rayuwa don tabbatar da adala.
Hakika akwai wadanda suka fasko baragurbin bagarar da batutuwan Baban-burin-huriyya, sannan akwai wadanda suka yi amannar amincewar da alamun ayyukan alkinta dukiyar kasa, ta hanyar farmakar masu kwashi-kwaraf, wadanda suka yi wa lalita karkaf, suka wawushe komai da komai kakaf. Kai ina ma jin cewa irin wnanan rukunin masu aika-aika Baba ke hankoron tsaurara matakan baje- na-mujiya a kansu.
Haurobiyawa, hakika akwai babbar bukatar da ta bijiro wajen ganin Baban-burin-huriya ya kafa tsandaurin tsandare tsiyatakun da ake tsuwurwurtawa a Jihar Zaman-fara, wadda ta koma ta fargaba. Saboda yawan kisan gilla da sace-sacen al’umma a yi ta garkuwar gagarakuwwa da su. Tunda manufar miyagu dai ba ta wuce gararambar gande-gande gararumar garar jar miya ba, to dolen-dole a tursasa kura ta amayar da abin da ta lakume ta handame ta hadidiye.
Babbar matsala dai da Gwamnatin Baban-burin-huriyya da Usainin-Babajo ta gada, ita ce burgar bugun bagun banke bobo da kwambon bokoko, lamarin da aka fi tsiwurwurtawa a Jihar Bararon-nono da wasu yankuna na Jihar Yawon-bebe, tare da daukacin yankin Arewatawan Arewa maso gabashin Haurobiya.
Lallai lokaci ya yi da kowa zai bayar da tashi gudumar gundumar gudunmawar garkuwar tsaurara tsarin tsaro a fadin Haurobiya.
’Yan makaranta mu yi karatun ta-natsu, kada mu karke da mutsu-mutsu, ko mu zo muna ta tsuwwa tsu-tsu da yunkurin tashi tamkar tsuntsu. Kada mu bari ’yan ba ni na iya su rude mu, tuni mun fasko jirginsu. Lallai mu TANTANCE TSAKANIN TSABA DA TSAKUWA, wato bambancin TSANANI da TSANDARAR TSANDAURI!