Kotunan Amurka sun samu tsohon Shugaban Kasar, Donald Trump, da laifuka 91 da aka tuhume shi da aikatawa inda yake fuskantar barazanar daurin shekara 700.
Wannan ne dai karo na hudu da kotunan kasar ke samun shi da aika laifukan da take zarginsa masu alaka da tayar da rikicin zabe da sauran batutuwa.
- Nijar: Za mu dawo da Bazoum ta kowace hanya —Sojojin ECOWAS
- Soja 25 ’yan ta’adda suka kashe a Neja —Hedikwatar Tsaro
Kodayake ba lallai tsohon Shugaban ya kwashe daruruwan shekarun a gidan yari ba, amma a bayyane yake zai fuskanci hukuncin daurin.
Ko a ranar Litinin sai da wata kotun da ke zamanta a Jihar Georgia ta kasar ta sami Trump da wasu mutum 18 da laifukan tayar da tarzoma yayin zabukan kasar a shekara ta 2020.
Hakan dai na zuwa ne bayan tsohon shugaban, wanda aka taba tsigewa har sau biyu lokacin da yake kan mulki, ya fuskanci tuhume-tuhume daga ofishin babban mai shigar da kara na kasar, Jack Smith, a laifin kokarin sauya sakamakon zabe.
Kazalika, a watan Yuli ma an tuhumi Trump laifuka 32 kan laifin fallasa wasu muhimman takardun gwamnati a Jihar Florida, sannan aka tuhume shi da wasu guda shida a watan Agustan da ya gabata.
Sannan a watan Maris ma wata kotu a birnin Manhattan ta same shi da laifuka 34 saboda zargin alaka da wata mai fina-finan batsa, Stormy Daniels, gabanin zaben 2016.
Donald Trump, na jam’iyyar Repub;lican dai ya sha kasa a hannun Joe Biden na Democrat a zaben 2020, inda ya gaza kai bantensa a neman wa’adin mulkinsa na biyu.