A bisa wata sabuwar dokar tafiye-tafiye ta wucin gadi da za ta fara aiki daga ranar 24 ga watan Dasumba na bana zuwa 24 ga watan Yunin badi, dole al’ummar wasu kasashen Afrika 15 su biya kimanin dala dubu 15 kafin su iya samun bizar shiga kasar Amurka.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce shirin na watanni shida wanda zai shafi masu ziyartar kasar da kuma ’yan kasuwa, zai zama izina ga masu ketare lokacin zama a kasar sabanin yadda bizarsu ta kayyade.
- An tsige Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Gombe
- An kara wa ‘yan sandan da aka kashe a zanga-zangar #EndSARS matsayi
- Dan Najeriya ne ya kirkiro rigakafin COVID-19 a Amurka
Wannan sabuwar doka ta yi wa wasu kasashen duniya takunkumin shiga Amurka na daya daga cikin manufofin Shugaban Kasar mai barin gado, Donald Trump, wanda ya sha kaye a zaben kasar da aka gudanar a ranar 3 ga watan Nuwamba.
Sai dai zababben Shugaban Kasar Joe Biden, ya sha alwashin sauya galibin matakan shige da fice da Trump ya shimfida, duk da cewa kawo sauyin na iya daukar watanni ko ma shekaru.
Kasashen Afirkan da sabuwar dokar za ta shafa sun hada da; Angola da Burkina Faso da Chadi da Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo da Djibouti da Eritrea da Gambia da Guinea-Bissau da Liberiya da Libiya da Mauritania da Sudan da Sao Tome and Principe da Cape Verde da kuma Burundi.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, kasashen na daga cikin jerin kasashe 24 da sabuwar dokar za ta shafa inda ragowar suka hadar da; Afghanistan, Bhutan, Syria, Yemen, Iran, Laos, Burma, da Papua New Guinea.