✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon harajin Trump zai jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala — WTO

Hukumar ta ce harajin na iya ƙara ta'azzara harkokin tattalin arziƙi.

Shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana damuwa kan sabon harajin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya saka kan kayayyakin da ke shiga da su ƙasar daga ƙasashen duniya.

Wannan haraji ya haɗa har da kashi 14 cikin 100 na kayayyakin da ake shiga da su ƙasar daga Najeriya.

A cewar sanarwar da WTO ta fitar a ranar Alhamis, hukumar na nazari da bibiyar matakin domin fahimtar yadda zai shafi cinikayya da kuma ci gaban tattalin arziƙin duniya.

Okonjo-Iweala, ta ce wasu ƙasashe mambobin WTO sun nuna damuwa kan wannan lamari, inda suka buƙaci ɗaukar matakan rage illar hakan.

Harajin da Trump ya sanar ranar 2 ga watan Afrilu ya zo ne daidai lokacin da ƙasashe da dama ke ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziƙinsu daga tasirin rikicin Rasha da Ukraine, da kuma tasirin hauhawar farashi da ake fama da shi a duniya.

Me ƙasashe ke cewa kan sabon harajin?

Ƙasashe irin su China da Turai sun nuna rashin jin daɗinsu kan harajin Trump, inda China ta mayar da martani da nata sabon harajin.

A Najeriya kuwa, masana tattalin arziƙi sun fara fargabar cewa ƙarin harajin zai ƙara tsadar kayayyaki da kuma rage damar fitar da kaya zuwa ƙasashen waje.

Ƙungiyoyin cinikayya sun fara kira ga Amurka da ta janye harajin, domin gudun jefa ƙasashe masu tasowa cikin mawuyacin hali.

Wannan lamari na faruwa ne a daidai lokacin da Amurka ke cikin yanayin siyasa mai zafi, tun bayan da Trump ya sake ɗarewa karagar mulki a karo na biyu.