Tsohon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump, ya maka kafar yada labarai ta CNN a kotu yana neman ta biya shi diyyar Dala miliyan 475 kan neman bata masa suna.
Trump ya maka CNN a kotu ne ranar Litinin, bisa zargin ta da neman bata masa domin yakar burinsa na neman takarar shugaban kasar Amurka a zaben 2024.
- Tallar Crypto ya ja wa tauraruwar shirin talabijin tarar Dala miliyan1.26
- Ambaliyar Jigawa: Sufurin kwale-kwale ba bisa ka’ida ba na kara cin rayuka
“CNN na neman yin amfani da shuhurarta da yadda mutane suka aminta da ita wajen bata wa mai kara suna a idon masu kallo da masu karatu da nufin goga masa kashin kaji a siyasance,” in ji takardar karar da lauyansa ya shigar a gaban kotun Yankin Florida.
Ya ci gaba da cewa, “Daga cikin dabarun na CNN akwai shirin amfani da labaran karya da kuma kiran Trump da miyagun siffofi da lakabobi kamar ‘mai nuna wariya’, ‘dan koron Rasha’, ‘mai tayar da tarzoma’, da Hitler da suaransu.”
Trump, dai na da dangantaka mai tsami da CNN da wasu manyan kafofin yada labaran Amurka irin su The New York Times a lokacin shugabancinsa.
A lokacin da yake shugaban kasa, Trump ya rika zargin su da yada labaran karya tare da yakar su a kafofin sada zumunta.