Kungiyar Tottenham ta hada wa kocinta Nuno Espirito Santo kayansa, bayan wata hudu yana jan ragamar aikin horar da ’yan wasan kungiyar.
Hakan dai na zuwa ne bayan da kungiyar ta sha kashi har gida a karawar da ta yi da Manchester United wanda aka ta shi ci 3-0 a wasan mako na 10 a gasar Firimiyar Ingila.
Wannan wasan dai shi ne cikon na biyar da Tottenham ta sha kashi a cikin bakwai da ta fafata a babbar gasar Ingila a bana.
A yanzu haka dai kungiyar tana ta takwas a teburin Premier da tazarar maki 10 tsakaninta da Chelsea, wadda ke saman teburin kakar bana.
Nuno Espirito dan kasar Portugal mai shekara 40 ya karbi aikin horar da Tottenham a watan Yuni, bayan kaka hudu da ya yi a Wolverhampton.
A watan Yunin ne dai aka nada Nuno a matsayin kocin kungiyar na dindindin kan kwantaragin shekaru biyu bayan ta raba gari da tsohon kocin Chelsea, Manchester United, Real Madrid da Inter Milan, Jose Mourinho.
Tottenham ta ce za ta sanar da wanda zai maye gurbin Nuno nan gaba domin jan ragamar kungiyar.
Sai dai ana rade-radin tsohon kocin Inter Milan da Chelsea, Antonio Conte ne zai maye gurbinsa kamar yadda Jaridar Goal ta wallafa.