✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

… Tornadoes ta dakatar da ’yan kwallonta biyu

Kulob din Neja Tornadoes da ke Minna wanda ya fara shirin tunkarar kakar wasa ta bana a gasar firimiya da ake sa ran farawa  jibi…

Kulob din Neja Tornadoes da ke Minna wanda ya fara shirin tunkarar kakar wasa ta bana a gasar firimiya da ake sa ran farawa  jibi Lahadi, ta bayar da sanarwar dakatar da biyu daga cikin ’yan kwallonta.
’Yan kwallon biyu da aka dakatar su ne  Chinedu Nwaze da kuma Lukman Mohammed.  An dakatar da ’yan kwallon ne a sansanin horar da su da ke Ilorin a shekaranjiya Laraba bayan kulob din ya neme su kasa ko sama, bayan sun bar sansanin horarwar ba tare da izini ba.
Shi dai Lukman Mohammed wanda yake kwallo a gaba (striker) da kuma Nwaze da ke buga kwallo a bangaren baya (defender) kulob din ya neme su ne jim kadan bayan ya kammala wasan sada zumunta da kulob din Kwara United da ke Ilorin, amma abin mamaki sai aka neme su sama ko kasa ba tare da an same su ba.
An ce ’yan kwallon sun yi karyar ba su da lafiya a ranar Talatar da ta wuce ne inda a washegari Laraba kuma suka bar sansanin horar da su ba tare da izini ba.
daya daga cikin jami’in kulob din Neja Tornadoes George Daniya ya ce tuni kulob din ya dakatar da su kuma nan gaba kadan za a yi nazarin hukuncin da ya dace ga ’yan kwallon don ya zama darasi ga saura.
 Kulob din ya gargadi sauran kulob da ke kasar nan musamman wadanda za su yi wasa a rukunin firimiya da kada su kuskura su kulla wata yarjejeniya da wadannan ’yan kwallo, kuma duk kulob din da ya yi haka to ya kuka da kansa.
Daniya ya ce ya yi mamakin yadda ’yan kwallon suka nuna halin rashin da’a musamman Lukman Mohammed wanda ya kasance yana daya daga cikin tsofaffin ’yan kwallon da kulob din yake ji da su.