A ranar Alhamis 23 ga watan Yuli ake binne mace ta farko mai tuka jirgin sama na yaki a Najeriya, Tolulope Arotile.
Ga wasu daga cikin hotunan yadda ake shirye-shiryen jana’izar da za a yi wa Tolutope a Makabartar Sojoji ya ke Abuja:

‘Yan uwan marigayiya Flying Tolulope Arotile a lokacin bikin jana’izarta a Makabartar Sojoji da ke Abuja.

‘Yan uwarta tare da limaman addinin Kirista a lokacin jana’izar a Abuja.
Hoto: Felix Onigbinde

Sojoji dauke da gawar Tolulope Arotile za su sanya ta a makwancinta.
Hoto: Felix Onigbinde

Shugaban Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar yana mika tutar Najeriya ga ‘yar uwar mai rasuwar bayan an binne ta. Hoto: Felix Onigbinde

‘Yar uwar Tolupe a wurin jana’izarta.
Hoto: Felix Onigbinde

Bankwanan soji ga marigayiyar ta hanyar yin harbi sau 21 a makabartar sojoji, Abuja. Hoto: Felix Onigbinde

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Abayomi Gabriel Olonisakin yana ajiye furen bankwana da karramawa a jana’izar Tolulope.
Hoto: Felix Onigbinde.