Ministan Ayyuka, Dave Umahi, ya ce duk titunan da ake ginawa a Najeriya yanzu ba za su shekara bakwai ba tare da sun lalace ba.
Da yake ganawa a Abuja da kamfanonin da Gwamnatin Tarayya ta ba wa ayyukan, Umahi ya zarge su da amfani da kayan aiki marsa inganci, wanda ya ce tsabar cuta ce.
- Gwamnatin Kano za ta yi karar alkalin zaben gwamna kan cin mutuncin Kanawa
- DAGA LARABA: Dalilin da ba za mu bari likita na miji ya duba matanmu ba
Ya bayyana musu cewa ya bi titunan da suke ginawa domin ganin hakakin halin da suke ciki, kuma “ban gamsu da taswirar aikin titin Abuja-Kaduna-Zaira- Kano ba.
“Abin da na gani a tinunan da ake ginawa a titunan da ke yankin Arewa ta tsakiya ma ya bakanta min rai, ban gamsu da abin da na gani ba.”
Don haka ya ce wanda ya rasu a sanadiyyar rashin ingancin tituna, to alhakin yana wuyan wuyan ’yan kwangilar da jami’an ma’aikatarsa da suka yi sakaci da aikinsu na sa ido a kai.
Ya ce, “Babu titi daya cikin wadanda ake ginawa yanzu da zai shekara 7 bai lalace ba. Shin haka za mu ci gaba, duka bayan shekara 10 sai mun kashe kudi wajen gyaran ko sake gina titunan?
“Na bi titin Abuja-Lakwaja-Benin, wanda yanzu haka gaba dayansa ana aikin ginawa, amma kashi nawa dinsa ne ke da kyau?
“Da na bi titin Abuja zuwa Lokoja na dangana da Benin sai da na yi kwalla saboda irin bakar wahalar da ga matafiya na sha.
“Awa 14 muka yi daga Abuja zuwa Benin, kuma gara da na bi titin da kaina na ga irin wahalar da ake sha. Shugaba Tinubu ya umarce ni in bi titunan inga hakikanin halin da suke ciki, in gaya masa gaskiyar lamarin.”
A cewar Ministan “Na je yankin Kudu maso Yamma, nan ba ban ji dadin abin da na gani ba, duk da cewa na ba su maki 80 cikin 100.”
Don haka ya ce “Dole sai Shugaban Kas aya dauki kwakkwaran mataki kan matsalar, idan ba haka ba, burin samar da ci gaba a kasar nan ba zai cika ba.
“Ya za a yi ’yan kwangila su iya aikin da ake kara musu alhali idan suka tura takardun neman izini hukumar sayayyar kayayyakin gwamnati, sai a shafe wata shida takardun ba su fito ba.”
Ministan ya ce karya ake yadawa domin bata masa suna, cewa farashin buhun siminti zai kai N9,000 idan gwamnati ta koma gina titunan kankare.