✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tirela ta murƙushe ɗalibai 2 har lahira a Kogi

Tirelar ɗauke da kaya wacce birkinta ya ƙwace ta murƙushe Keke NAPEP, inda nan take ta kashe biyu daga cikin fasinjojin.

Wasu ɗalibai mata biyu sun mutu tare da samun wasu raunuka da dama a wani haɗari da ya afku a Felele da ke ƙarshen babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja a jihar Kogi.

An samu rahoton cewa haɗarin ya afku ne da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar Juma’a, a kusa da rukunin gidajen ma’aikatan Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kogi, a Lokoja, inda wata tirela ɗauke da kaya birkinta ya ƙwace ta murƙushe babur mai ƙafa uku (Keke NAPEP), inda nan take ta kashe biyu daga cikin fasinjojin.

Katin shaidar da aka samu na ɗaya daga cikin ɗaliban mata da suka rasu yana ɗauke da sunan, Covenant Omolola Isaac, a Tsangayar Nazarin Ƙasa na Jami’ar Tarayya Lokoja.

Ɗalbar ta biyu tana da sunan Abu Taiwo Abimbola, Sashen Nazarin Kimiyya da Fasaha, daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi, Lokoja.

Marigayi Abimbola, wacce ita dai ɗalibar matakin karatun HND II a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar, a Lokoja, tana kan hanyarta ta zuwa yin jarrabawa da ake ci gaba da yi a makarantar a lokacin da lamarin ya faru.