Wasu mutum uku sun rasa rayukansu yayin da wata tirela dauke lemuka na kamfanin Coca-Cola ta bi ta kansu a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Kamfanin Dillacin Labarai (NAN) ya ruwaito cewar mutanen uku da suka riga mu gidan gaskiya na haye na a kan wani baburin dan acaba.
- Maganin gargajiya ya yi ajalin mutum 10 ’yan gida daya
- Buhari ya kafa kwamitin rage radadin talauci a Najeriya
Wani mai suna Mista Joel Idowu, da hadarin ya faru a kan idonsa, ya ce motar ta murkushe mutum ukun yayin da babur dinsu ke kokarin wuce motar, a daidai gidan mai na Boya.
Idowu ya kara da cewa wasu fusatattun matasa sun yi yunkurin kone tirelar a yayin da ’yan sanda suka yi gaggawar tarar hanzarinsu.
Tuni dai tarzoma ta lafa a yankin bayan ’yan sanda sun dauke motar zuwa ofishinsu don gudanar da bincike, inda kuma aka mika gawarwakin mutanen zuwa wani asibiti da ke kusa.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa reshen Jihar, Misis Uche Chukwurah ta tabbatar da faruwar lamarin.
Chukwurah ta ce hadarin wanda ya ritsa da mutum biyar, ya yi ajalin mutum yayin da ragowar biyun suka samu rauni.
Ta ce ana zargin shanyewar birkin babbar motar ne silar aukuwar hadarin.
Sannan ta kara da cewar wanda suka samu rauni na asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan, inda suke samun kulawa.