✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu zai tafi Chadi ranar Alhamis

Wannan ne karon farko da Tinubu zai ziyarci Chadi tun bayan zamansa Shugaban Nijeriya.

Shugaba Bola Tinubu zai tafi Chadi ranar Alhamis domin halartar bikin rantsar da Mahamat Déby a matsayin shugaban ƙasar.

Mai bai wa shugaban ƙasar shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Ajuri ya ce shugaba Tinubu zai bar Abuja ranar Alhamis zuwa birnin N’Djamena na Jamhuriyar Chadi domin bikin rantsar da shi.

A farkon wannan watan na Mayu ne aka ayyana Mahamat a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar 6 ga wata.

Sakamakon hukumar gudanar da zaɓe ta ƙasar Chadi a watan Mayu ya nuna cewa Deby ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasar da fiye da kashi 61 cikin 100 na kuri’un da aka kaɗa.

Mahamat Deby ya doke abokin babban hamayyarsa, Firayim Minista Succes Masra, wanda ya samu kashi 18.5 cikin 100.

Sai dai ’yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaɓen.

Aminiya ta ruwaito cewa wannan ne karon farko da Tinubu zai je Chadi tun bayan zama Shugaban Nijeriya a watan Mayun 2023.

“Manyan jami’an gwamnati za su yi wa shugaban rakiya kuma za su koma gida bayan kammala bikin,” in ji sanarwar da Ngelale ya fitar.