Shugaba Bola Tinubu zai gana da gamayyar ƙungiyar ƙwadago a Abuja a gobe Alhamis domin ci gaba da tattaunawa kan mafi ƙarancin albashin ma’aikatan Nijeriya.
Hakan na zuwa ne kimanin wata gudu bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da cewar zai aike wa Majalisar Tarayya ƙudirin akan mafi ƙarancin albashi domin zartarwa.
- Kawu Sumaila ya miƙa ƙudirin ƙirƙiro sabuwar jiha daga Kano
- Ganduje da matarsa za su bayyana a kotu kan zargin almundahana
Wata babbar majiyar ‘yan kwadago ta shaida wa tashar talabijin ta Channels cewar, Tinubu ya gayyaci shugabannin ƙungiyar ƙwadago ta NLC da takwarorinsu na TUC zuwa ganawar da ake sa ran za ta wakana a Fadar Aso Villa da ke birnin Abuja.
Ana sa ran Tinubu zai yanke matsaya kan tayin Naira dubu 62 da ɓangaren gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu suka gabatar da kuma na Naira dubu 250 da ɓangaren ‘yan kwadagon ya gabatar.
Taron na ranar Alhamis na zuwa kimanin wata guda bayan da Tinubu a jawabin da ya gabatar a Ranar Dimokuraɗiyya, cewa nan ba da jimawa ba za a aike da ƙudiri akan mafi ƙarancin albashi daga ɓangaren zartarwa zuwa ga Majalisar Tarayya domin a zartar da shi.
Ana iya tuna cewa, a ranar 25 ga watan Yunin da ya gabata ne, Majalisar Zartarwa karkashin jagorancin Shugaba Tinubu ta jingine ci gaba da nazari da tattaunawa akan batun mafi ƙarancin albashin domin ba da damar faɗaɗa tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
Kwanaki biyu bayan hakan, Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima suka gana da gwamnonin jihohin Nijeriya 36 da ministoci akan batun sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan kasar, yayin karo na 141 na taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa.