✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu zai ƙara fiye da N6trn a Kasafin Kuɗin 2024

Za a yi amfani da kuɗin wurin bunƙasa manyan ababen more rayuwa a fannin ilimi da kiwon lafiya.

Shugaban Bola Tinubu ya buƙaci ƙara Naira tiriliyan 6 da biliyan 200 a cikin Kasafin Kuɗin Nijeriya na 2024.

Hakan na ƙunshe ne cikin buƙatar da shugaban ya miƙa wa Majalisar Dattawa yana neman ta yi gyara kan dokar Kasafin Kuɗin bana da ta harkokin kuɗaɗe ta bara ta hanyar ƙara fiye da Naira tiriliyan a cikin kasafin kudin bana.

A cikin wasiƙar, shugaban ya bayyana cewar matakin ya dace da sashe na 58, ƙaramin sashe na 2 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Wasiƙar da Shugaban Majalisar Dattawan Sanata Godswill Akpabio ya karanta, ta ce “A nan ina gabatar wa Majalisar Dattawa da wannan ƙuduri domin ta yi nazari tare da zartar da shi.

“Kudirin dokar kashe kuɗaɗe ta bana ya nemi a yi gyara akan ainihin dokar da nufin samar da naira tiriliyan 3 da biliyan 200 domin aiwatar da ayyukan raya kasa ƙarƙashin shirin “sabunta fata” (Renewed Hope) tare da sauran muhimman ayyukan raya ƙasar da ke gudana a faɗin ƙasar nan.

“Sannan naira tiriliyan 3 domin samar da ƙarin kuɗaɗen da aka na kashe yau da kullum, waɗanda wajibi ne domin gudanar da harkokin kashe kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya yadda ya dace, kuma ake sa ran samu daga asusun kuɗin shiga na Gwamnatin Tarayyar.”

Tinubu ya kara da cewa ana buƙatar yin kwaskwarima kan dokar harkokin kuɗi ta 2023 ne domin cazar haraji daga irin ribar da bankunan suka samu a hada-hadar musayar kuɗaɗen kamar yadda bayanan hada-hadar kudadensu ta bara suka nuna.

Tinubu ya ci gaba da cewar an yi haka ne domin samun kuɗaɗen gudanar da ayyukan raya ƙasa da bunkasa ilimi da kiwon lafiya da tsare-tsaren sanya walwala a zukatan al’umma.