Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya zama sabon Shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS.
An sanar da shi ne a yayin taron kungiyar na 63 wanda ake yi a Guinea Bissau a yau Lahadi.
- Gobarar Igiyar Leko ta yi ajalin Almajirai 3 a Adamawa
- Tinubu ya ziyarci dakarun Najeriya a Guinea Bissau
Tinubu ya karbi jagorancin kungiyar ne daga hannun Shugaban na Guinea Bissau, Umaro Embalo.
Wannan ne karo na farko da Tinubu ya halarci taron na ECOWAS tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
A makon jiya ne Shugaba Tinubu ya karbi bakuncin Shugaba Embalo a birnin Legas, inda ya ce sun ci abinci tare kuma “mun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafe mu.”
A wancan lokacin, Tinubu ya ce babban burinsa shi ne ya sake mayar da kasar jagora ga sauran kasashen nahiyar Afirka.