✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobarar Igiyar Leko ta yi ajalin Almajirai 3 a Adamawa

Tabbas wannan lamari mukaddari ne daga Allah kuma babu makawa sai ya faru.

Wasu Almajirai uku sun riga mu gidan gaskiya sanadiyyar gobarar igiyar leko a Tsangayar Sabon Pegi da ke gundumar Shagari a Karamar Hukumar Yola ta Kudun Jihar Adamawa.

Bayanai sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:40 na daren ranar Juma’a yayin da Almajiran suka kunna igiyar lekon domin kore sauro a dan akurkin da suke kwana.

Malam Abubakar Usman, Shugaban Tsangayar, ya shaida wa Aminiya cewa Almajiran uku sun yi gamo da ajali sanadiyyar igiyar lekon da galibi suka saba amfani da ita domin su yi barci cikin kwanaciyar hankali ba tare da kuka ko cizon sauro ya addabe su ba.

Ya bayyana cewa Almajiran da lamarin ya rutsa da su sun hada da wani Ismaila Muhammadu mai shekaru 12, sai Yusuf Abubakar mai shekaru 13 wadanda suka mutu nan take.

Sai dai ya ce cikon na ukun, Mustapha Ahmadu mai shekaru 17, ya mutu washegari Asabar a Asibitin Koyarwa na Modibbo Adama da ke Yola.

Yadda aka yi zaman makoki bayan rasuwar Almajiran

“Da misalin karfe 11:40 ma dare ne bayan duk Almajiran sun kwanta barci. Sai daya daga cikinsu ya zo yana kuka.

“Muna zuwa sai muka riski daya daga cikin bukkokin na ci da wuta.

“A kokarin kashe wutar ne muka yi arba da gawar Almajirai biyu a cikin bukkar da kone kurmus.

Yadda bukka mai kama da akurki ta kone kurmus a Tsangayar

Aminiya ta ruwaito Malam Abubakar yana neman agajin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da suka kawo musu daukin gina wa Almajiran matsugunni da azuzuwa da bandaki don ganin irin tsautsayi bai sake aukuwa ba.

Mahaifin daya cikin mamatan, Muhammad Bello Sabon Gari, ya bayyana lamarin a matsayin mukaddari daga Allah.

Wata daga cikin bukkokin Almajiran.

A cewarsa, “na yarda da Allah kuma Shi Ya kaddara faruwar wannan lamari kuma babu makawa sai ya faru.”

Ya jajanta wa malamin Almajiran tare da neman ya dauki dangana.

A nasa jawabin, Garba Ayuba Faranga, wani mahaifin daya daga cikin mamatan, ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da aukuwar lamarin.

Sai dai Faranga ya kuma bayyana yadda wahalar rayuwa ta hana shi aikowa dansa abun guzuri tun bayan da ya turo shi almajaranci.

Tuni dai aka binne mamatan a bisa koyarwar addinin Islama.