Ana fargabar cewa aƙalla yara 19 ne suka mutu sakamakon ɓullar wata cuta da ake zargin ƙyanda ce a Karamar Hukumar Mubi ta Arewa da ke Jihar Adamawa.
Da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN, kwamishinan lafiya na jihar, Felix Tangwami ya ce sama da yara 200 yanzu haka sun kamu da cutar a ƙaramar hukumar.
- Naɗin sarautar Hausawa ta haddasa saɓani da fadar Oba na Benin
- Ya nemi ’yan Arewa su mara wa PDP baya a zaɓen Gwamnan Edo
Ya ce a ranar Asabar ma an samu bullar cutar a Yola babban birnin jihar, abin da ya janyo aike wa da magunguna da kuma ma’aikatan lafiya ga kauyukan da abin da ya shafa.
Ya yi alƙawarin za a yi maza a garzaya da yaran da suka kamu zuwa asibitoci.
Kwamishinan ya ce za a aika da jami’an lafiya ƙaramar hukumar Mubi da Gombi inda aka ƙara samun bullar cutar.
Ya alaƙanta lamarin da sakacin iyaye na rashin tabbatar da an yi wa ’ya’yansu allurar rigakafin cutar.
Ƙyanda dai wata cuta ce da take yaɗuwa ta yi illa kuma musamman tsakanin yara ƙanana.
Daga cikin illar da take haifarwa akwai makanta da kumburin ƙwaƙwalwa da gudawa da numfashi da ƙyar.