Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim, wanda ya rasu a kasar Saudiyya.
Wannan na cikin sanarwar da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Lahadi.
- Sojoji sun fatattaki ‘yan bindiga, sun ceto mutum 4 a Taraba
- INEC ta dakatar da jami’inta kan batan sakamakon zabe a Filato
“A madadin Gwamnatin Tarayya ina mika sakon ta’aziyyata ga ’yan uwa da iyalan Sanata da gwamnati da kuma al’ummar Jihar Yobe.
“Tsohon Gwamna Ibrahim aboki ne kuma babban shugaba ne wanda ya yi wa al’ummar Yobe hidima da kwazo a lokacin da ya yi harkar siyasa.
“A matsayinsa na wanda ya yi Sanata na tsawon shekara 12, kwarewarsa ta taimaka wajen jagoranci a Majalisar Dokoki ta Kasa.
“Al’umma za su tuna shi a matsayin jajirtaccen shugaba da ya yi hidima wajen gina rayuwar mutane da kasa baki daya,” in ji Tinubu.
Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya jikan marigayin da rahama.
Tsohon gwamnan ya rasu ne, a ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin Makkah kasar Saudiyya, bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Sakataren Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mamman Mohammed, ya tabbatar da rasuwar.
Ya ce za a yi jana’izar marigayin a Saudiyya, inda kuma za a yi zaman makokin rasuwar a Jihar Yobe.