✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tinubu ya yi min tayin kujerar Sanata —Wike

Wike ya ce ya yi watsi da tayin Tinubu da sauran jam'iyu da ke zawarcin sa domin cin zaben 2023

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya yi masa alkawarin takarar Sanata idan ya goya masa baya a zaben 2023.

Ya bayyana cewa bayan Tinubu, jam’iyyun siyasa da dama da suke ganin zai taimaka musu samun nasara a zaben 2023, sun yi zawarcin sa, amma ya yi biris da tayinsu.

Ya ce ya ki amince da tayin Tinubu na kujerar Sanata, kasancewar tun farko fom din kujerar shugaban kasa ya saya, ba takarar Sanata ba.

A cewarsa, daga cikin jam’iyyun da suka yi zawarcin sa, har da Jam’iyyar Labour, saboda sanin muhimmancin sa da kuma yadda suke ganin zai taimaka musu wajen samun nasara.

Gwamnan Ribas din ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a tashar talabijin ta TVC.

Wike, wanda ke zargin jam’iyyarsa ta PDP da cin amanarsa, ya zargi Shugaban Jam’iyyar, Iyorchia Ayu, da kwadayin samun kujerar Sakataren Gwamnatin Tarayya idan Atiku Abubakar ya ci zaben 2023.

A cewarsa, wannan ne ya sa Ayu ya taimaka wajen ganin bai samu nasara a zaben dan takarar shugaban kasa da jam’iyyar ta gudanar ba.

A halin yanzu dai, Wike da magoya bayansa sun janye daga kwamitin yakin neman zaben Atiku, suna cewa ba za su goyi bayan Atiku a zaben mai zuwa ba sai Ayu ya sauka daga mukaminsa.

Atiku dai ya mayar da martani cewa ba zai sa Ayu ya yi murabus ba, wannan ra’ayin Ayi ne, idan ya ga dama.

Suke ya ce an riga an gama rabon mukaman Gwamnatin Tarayya ga ’ya’yan jam’iyyar su ta PDP, ciki har da wanda zai zama Shugaban Majalisar Dattawa, idan Atiku ya ci zaben mai zuwa.