Shugaban Kasa Bola Tinubu yanzu haka yana gana wa da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da takwaransa na Ribas, Nyesom Wike a Fadar Shugaban da ke Abuja.
Tsofaffin Gwamnoni biyun dai na cikin mutanen da Shugaba Tinubu ya aike da sunansu ga Majalisar Dattijai da nufin nadawa Ministoci.
- Juyin mulki: Sanusi ya gana da Shugaban mulkin sojan Nijar
- Masu aikin shara sun ci Naira tiriliyan daya a caca
To sai dai majalisar ta ce an tabbatar da nadin Wike, amma na El-Rufa’i har yanzu akwai saura saboda wani rahoton tsaro da ake kokarin kammalawa.
Sun dai isa fadar ce ranar Laraba daban-daban.
Wike ne dai ya fara isa da misalin karfe 1:40 na rana, yayin da El-Rufa’i ya isa da karfe 2:00 na rana.
Majiyoyi a fadar sun ce tattaunawar ba za ta rasa nasaba da kokarin ganin majalisa ta tabbatar da nadin El-Rufa’in ba.