Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Muhammad Babangida, ɗan tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, a matsayin sabon Shugaban Bankin Manoma (BOA).
Shugaban, ya kuma amince da naɗin wasu mutane guda bakwai a matsayin shugabanni da jagororin hukumomin gwamnati daban-daban.
- Ɗan Majalisar Wakilai ya tallafawa fiye da mutum 3,000 a Kaduna
- Dantata mutum ne mai tausayi da ƙaunar Najeriya — Tinubu
Wannan na cikin wata sanarwa, Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar.
“Wasu daga cikinsu za su kasance shugabanni ko daraktoci na hukumomin tarayya.”
Muhammad Babangida yana da shekaru 53.
Ya yi karatu a fannin Gudanar da Kasuwanci a Jami’ar Turai da ke Montreux, Switzerland, sannan ya samu digirin digirgir a fannin Hulɗa da Jama’a da Sadarwar Kasuwanci.
A shekarar 2002, ya halarci shirin horo na manyan shugabanni kan yadda ake tafiyar da hukumomi a Makarantar Kasuwanci ta Harvard.
Sauran naɗe-naɗen da Shugaba Tinubu, ya yi sun haɗa da Lydia Kalat Musa daga Jihar Kaduna a matsayin shugabar Hukumar Harkokin Mai da Iskar Gas.
Jamilu Wada Aliyu daga Jihar Kano, a matsayin sabon shugaban Hukumar Bincike da Ci gaban Ilimi ta Ƙasa.
Honarabul Yahuza Ado Inuwa, shi ma daga Kano, an naɗa shi shugaban Hukumar Daidaita Kayayyaki.
Sanusi Musa (SAN) daga Kano, zai shugabanci Cibiyar Wanzar da Zaman Lafiya da Warware Rikice-rikice.
Farfesa Al-Mustapha Alhaji Aliyu daga Jihar Sakkwato an naɗa shi Darakta Janar na Hukumar Haɗin Gwiwar Fasaha a Afirka.
Sanusi Garba Rikiji daga Jihar Zamfara shi ne sabon Darakta Janar na Ofishin Tattaunawar Kasuwanci na Najeriya.
Sai Hajiya Tomi Somefun daga Jihar Oyo, a matsayin sabuwar Manajan Darakta na Hukumar Raya Wutar Lantarki da Ruwa (HYPPADEC).
Dokta Abdulmumini Mohammed Aminu-Zaria daga Jihar Kaduna, ta zama Darakta na Hukumar Kula da Albarkatun Ruwa a Najeriya.
Wannan jerin naɗe-naɗe yana cikin matakan da Shugaba Tinubu ke ɗauka domin bunƙasa shugabanci a manyan hukumomin gwamnati.