✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya naɗa shugabannin Hukumar Raya Arewa Maso Yamma

Matakin na zuwa ne bayan sanya hannu kan dokar da ta amince da ƙirƙiro sabuwar hukumar.

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji daga Jihar Kano a matsayin shugaban Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma.

Wannan na zuwa ne a yayin da Shugaba Tinubu ya miƙa sunayen shugabannin majalisar gudanarwar sabuwar hukumar da ke da alhakin raya Arewa maso Yammacin ƙasar zuwa ga Majalisar Dattawa domin amince wa naɗinsu.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ya ce matakin na zuwa ne bayan sanya hannu kan dokar da ta amince da ƙirƙiro sabuwar hukumar.

Tun a ranar 24 ga watan Yuli ne dai Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar.

Mutanen da Shugaba Tinubun ya aike da sunayensu domin jagorantar sabuwar hukumar sun haɗa da Ambassada Haruna Ginsau daga Jihar Jigawa a matsayin Shugaban Majalisar Gudanarwar hukumar.

Sauran mambobin hukumar sun haɗa da Dokta Yahaya Umar Namahe (Sakkwato) da Aminu Suleiman (Kebbi) da Sen. Tijani Yahaya Kaura (Zamfara) Abdulkadir S. Usman (Kaduna) da Injiniya Muhammad Ali Wudil (Kano) da Shamsu Sule (Katsina) da kuma Nasidi Ali (Jigawa).

Sanarwar ta ci gaba da cewa ana sa ran sabbin shugabannin za su yi amfani da ƙwarewarsu wajen gina sabuwar hukumar.