✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya naɗa sabon Gwamnan CBN

Tinubu ya kuma naɗa Mataimakan Gwamnan Babban Bankin guda hudu.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Yemi Cardoso a matsayin sabon Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN.

Ya bayyana haka ne a sanarwar da mai magana da yawunsa Cif Ajuri Ngelale. ya fitar ranar Juma’a.

Olayemi Michael Cardoso ya maye gurbin Godwin Emefiele wanda Shugaba Tinubu ya dakatar daga mukaminsa kuma ake tuhumarsa da badakalar biliyoyin kudade.

A cewar Ngelale, wannan naɗin wanda ake sa ran Majalisar Dattawa za ta tabbatar da shi ya dace da sashe na takwas (1) na Kundin Dokar CBN da aka yi wa kwaskwarima a 2007.

Kazalika, Cif Ngelale ya ce Tinubun ya kuma naɗa Mataimakan Gwamnan Babban Bankin guda hudu.

Sabbin Mataimakan Gwamnan Babban Bankin da aka naɗa na tsawon wa’adin shekaru biyar sun haɗa da Mista. Emem Nnana Usoro da Mista. Muhammad Sani Abdullahi Dattijo da Mista Philip Ikeazor da kuma Dokta Bala M. Bello.

Ana iya tuna cewa, a watan Yunin da ya gabata ne Shugaba Tinubu ya naɗa Folashodun Adebisi Shonubi a matsayin Gwamnan riko na Babban Bankin Najeriya CBN bayan dakatar da Godwin Emefiele.