Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Kemi Nanna Nandap a matsayin Kwanturola-Janar ta Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS).
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale, ya fitar yana mai ce naɗin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga Maris, 2024.
- Taurarin Zamani: Umar Farouk (Shakaka)
- An bai wa kowanne gwamna N30bn ya rage tsadar rayuwa a jiharsa — Majalisar Dattawa
Misis Nandap za ta karɓi aiki daga hannun Misis Caroline Wura-Ola Adepoju, wadda wa’adinta zai ƙare a ranar 29 ga Fabrairu, 2024.
Kafin naɗa ta a matsayin Kwanturola-Janar, Nandap ita ce Mataimakiyar Kwanturolan-Janar mai kula da sashen hijira.
Sanarwar ta ƙara da cewa, shugaban ya yi hasashen cewa sabuwar shugabar Hukumar Shige-da-Ficen za ta faɗaɗa gyare-gyaren da ake yi a hukumar da samar da ingantacciyar hanyar yi wa ‘yan Nijeriya hidima cikin inganci da kwazo.
“Haka kuma sabuwar shugabar za ta karfafa tsaron ƙasa ta hanyar samar da ingantaccen tsaro a kan iyakokin ƙasa da kula da al’amuran baƙin haure,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.