✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya kunyata masu kyautata masa zato — Sarkin Yaƙin Yarbawa

Idan Tinubu bai gaggauta janye waɗannan munanan matakan ba, tabbas halin matsin da ake ciki a ƙasar nan zai ƙara munana.

Sarkin Yaƙin Yarabawa, Iba Gani Abiodun Adams ya caccaki Shugaba Bola Tinubu kan halin tsadar rayuwa da ƙasar ke ciki da cewa ya kunyata duk waɗanda suka kyautata masa zato.

Fitaccen mai fafutikar kare muradun Yarabawan wato Aare Ona Kakanfo ya buƙaci Tinubu ya mayar da tallafin man fetur da ya cire tun bayan hawansa kan mulki.

Cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ya rubuta mai taken “Shugaba Tinubu lokaci na tafiya” Adams ya buƙaci Tinubu da ya janye wasu matakai masu tsauri da gwamnatinsa ta ɓullo da su.

Ya ce ya rubuta wasiƙar ce a matsayinsa na ɗaya daga cikin ’yan Najeriya sama da miliyan 200 domin bayyana masa halin da ƙasar ke ciki.

Mista Adams ya kuma zargi shugabannin Nijeriya da suka gabata da jefa ƙasar cikin halin da take ciki.

“Maganar gaskiya ita ce, shugabanni da suka gabata, tun daga 1960, sun bai wa ’yan Najeriya kunya musamman ta hanyar shugabanci maras inganci da suka yi da kuma almubazzaranci da dukiyar ƙasa,” in ji Adams.

Ya ce “lokacin da Tinubu ya fara yaƙin neman zaɓen 2023, ’yan Najeriya da dama sun amince cewa a matsayinsa na ɗan dimokuraɗiyya, zai iya yin shugabanci nagari fiye da wanda ya gada Muhammadu Buhari, wanda a cewarsa a zamaninsa ne talauci da rashin tsaro ya ƙaru daga 2015 zuwa 2023.”

Sai dai Sarkin Yaƙin Yarabawan ya ce akasin haka suke gani yanzu tun bayan hawan Tinubu kan mulki.

“Al’amuran da suke faruwa a yanzu na nuna cewa fatan da mutane ke da shi game da kai ya dusashe.

“Don haka maganar gaskiya shugaban ƙasa ka bai wa ’yan Najeriya da dama kunya, waɗanda suka yi zaton cewa kai ne za ka fitar musu da kitse daga wuta.”

Ya kuma zargi shugaban ƙasar da ɓullo da matakan da suka tayar da farashin man fetur.

“A lokacin da ka zama shugaban Nijeriya, farashin man fetur yana ƙasa da naira 200, amma a yanzu ya haura naira 1,000.

“Haka ma a watan Mayun 2023, ana sayar da dala ƙasa da naira 740, amma a yanzu ta haura naira 1,600.”

Sarkin Yaƙin yaƙin Yarabawan ya kuma ce ya yi mamakin yadda shugaban wanda ke aiki da tsoffin na hannun damarsa lokacin da yake gwamnan Legas suka kasa fitar wa ƙasar da kitse daga wuta ta ɓangaren tattalin arziki.

“Manyan na hannun damanka a lokacin da kake Gwamnan Legas, Wale Edun [Ministan Kuɗi] da Yemi Cardoso [Gwamnan CBN] su ne dai ke kula da tattalin arzikin ƙasar>

“Waɗannan irin matakan tattalin arziki da tsare-tsare kuɗi suke ɗauka, kuma waɗanne irin bayanai suke yi maka a kullum da za su gamsar da kai cewa suna aikinsu yadda ya kamata?

“Ka sani cewa idan na kusa da kai ko hadimanka na faɗa maka cewa komai na tafiya daidai, to ina mai tabbatar maka da cewa maƙiyanka ne.

Ya kuma yi kira ga shugaban ƙasar ya janye ƙarin kuɗin man fetur da NNPCL ya yi a baya-bayan nan tare da janye duka matakan da ya ce sun janyo wa ƙasar faɗawa matsin tattalin arziki.

“Idan ba ka gaggauta janye waɗannan munanan matakan ba, to tabbas halin matsin da ake ciki a ƙasar nan zai ƙara munana.”

“Abin takaici a yau, daga Arewa zuwa Kudu, Gabas zuwa Yamma, yadda ake sace ‘yan Nijeriya, ana kashe wasu, ko da an biya kudin fansa, kai ka ce waɗannan ’yan ta’addan masu shan jini kwararo su ake yi cikin Nijeriya.”

Sarkin Yaƙin Yarbawan ya kwatanta gwamnatin shugaban ƙasa da zamanin mulkin kama-karya na Adolf Hitler a Jamus, yana mai cewa, “A cikin watanni 16 kacal da mulkinku, har yanzu kuna gaza cika alƙawuran da kuka ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.