✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya kawo rumfar zabensa

Jam'iyyar APC ce ta samu mafi yawan kuri'u a zaben shugaban kasa, majalisar wakilai da na sanata a rumfar.

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya lashe rumfar zabensa da ke Alausa a Jihar Legas.

Jam’iyyar APC ce ta samu mafi yawan kuri’u a zaben shugaban kasa, majalisar wakilai da na sanata a rumfar mai lamba 03 a unguar Oregun da ka , da gundumar Olusosun a Kamar Hukumar Ikeja.

A zaben sanata APC ta samu kuri’a 36, ZLP 2, PDP 4, sai ADC ta samu kuri’a daya.

APC ta samu kuri a 31 a zaben dan Majalisar Tarayya, PDP daya, LP 9 sai SDP mai kuri’a 1.