Shugaba Bola Tinubu ya karbi rahoton kwamitin fadar shugaban kasa a kan kiwon dabbobi da zummar samar da gyara da damammaki a bangaren.
Ana shirin kafa ma’aikar kula da dabbobi ne da nufin magance matsalar rikice-rikicen manoma da makiyaya da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya sanar da shirin samar da ma’aikatar domin magance matsaloli da sukayi katutu a bangaren.
Bayo Onanuga ya ce shugaban kasan ya karbi rahoton kwamitin aiwatar da sauye-sauyen kiwon dabbobi ne daga hannun mataimakin shugaban kwamitin, Farfesa Attahiru Jega, a fadarsa da ke Abuja, ranar Alhamis.
- An jefa mu cikin tashin hankali da rufe sansanonin ambaliya —’Yan gudun hijira
- Gwamnatin Kano ta Soke Jami’ar Sa’adatu Rimi
Tinubun ne dai shugabantar kwamitin, amma kuma, Farfesa Jega, wanda tsohon shugaban hukumar zabe na kasa (INEC), ke jagorantar lamurran da suka gudana.
Daga cikin ayyukan da aka dora wa kwamitin, akwai batun samar da hanyoyin kafa ma’aikatar kula da dabbobi.