Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da Majalisar Tattalin Arzikin ta Kasa (NEC).
An kaddamar da majalisar ce karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima a zauren majalisar da ke fadar Shugaban Kasa da ke Abuja da safiyar Alhamis.
- Chukkol ya maye gurbin Bawa a matsayin Shugaban EFCC na rikon kwarya
- Cire Tallafi: Majalisar Wakilai ta bukaci Tinubu ya fito da hanyoyin rage radadi
Kaddamarwar ta samu halartar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume da dukkan Gwamnonin Najeriya 36.
Da yake jawabi, shugaban ya bukaci Gwamnonin da su hada kai da Kananan Hukumomi wajen bunkasa ababen more rayuwa cikin gaggawa duba da irin kalubalen da al’ummar kasar nan ke fuskanta.
“Ni da ku muka nemi wannan matsayi. Mun yi yakin neman zabe. Mun yi rawa don samu wannan nasara. Don haka, ba mu da dalilin yin korafi. ’Yan kasar nan suna bayanmu. Suna son gyara kuma cikin kankanin lokaci. A matsayinku na masu ruwa da tsaki…. Hadin kai ba laifi ba ne. Don haka mu yi aiki tare.”