Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya gana da shugabannin jam’iyyar APC na Jihar Kano a fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock da ke Abuja.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ne, ya jagoranci tsohon mataimakinsa kuma dan takarar jam’iyyar a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, 2023 Nasir Yusuf Gawuna.
- NAJERIYA A YAU: Za A Yi Wa Masu Sayar Da Rake Katin Shaida A Jihar Bauchi
- ’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka 10 a Kaduna
Sauran shugabannin jam’iyyar da suka halarci taron sun hada da: Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin; Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo; Karamar Ministar Babban Birnin Tarayya, Mariya Mahmoud Bunkure; Dan Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Bichi.
Sauran sun hada da Shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar, Murtala Sule Garo da kuma tsohon dan majalisar wakilai daga jihar, Hafiz Kawu.
Wannan dai na zuwa ne bayan mako guda da kotun koli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, a matsayin halastaccen gwamnan jihar.
Har bayan kammala taron da shugabannin APC na Kanoa, suka yi da Shugaba Tinubu ba a bayyana makasudin ziyarar tasu ba.
Amma hakan ba zai rasa nasaba da rashin nasarar da jam’iyyar mai mulki ta yi a kotun koli kan shari’ar zaben gwamnan jihar ba.
Idan za a tuna, a baya kotun sauraren kararrakin zabe da kotun daukaka kara sun kori Gwamna Yusuf tare da ayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.
Hakan ne ya sanya shugabannin jam’iyyar jihar fara shirye-shiryen karbar mulki, amma aka samu akasin hakan a kotun koli, inda ta dawo da Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar.