✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka 10 a Kaduna

Giwa dai na daya daga cikin kananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro a Arewa maso Yamma.

’Yan bindiga sun tarwatsa al’ummar kauyuka 10 da ke zaune a yankin Kidandan na Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Giwa dai na daya daga cikin kananan hukumomin da ke fama da matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

Aminiya ta ruwaito cewa, wasu daga cikin mazauna garuruwan da ta’adar ’yan bindigan ta tilasta musu yin kaura, sun koma ne babban garin Kidan da sauran yankunan da ke makwabtaka masu aminci a karamar hukumar.

Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Tunburktu, Hayin Dabino, Mugaba, Nasarawan Hayin Doka, Dokan Yuna, Doka, da Hayin Teacher.

Kansilan unguwar Kidandan, Abdullahi Ismail, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya koka da cewa a cikin makonni uku da suka gabata sojoji suna gudanar da ayyuka a kewayen yankin amma har yanzu ‘yan bindigar na ci gaba da kawo wa al’ummar farmaki.

Wani shugaban al’ummar, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce mazauna kauyukan da suka rasa matsugunansu sun bar kayan abincinsu da gidajensu saboda barazanar da ‘yan fashin dajin ke yi rayuwarsa da dukiyoyinsu.

Ya kuma bayyana cewa a ranar Talatar da ta gabata sojojin da ke sintiri a yankin sun kashe kusan shida daga cikin ‘yan bindigar.

Ya kara da cewa, duk da cewa mazauna yankin sun ji dadin kashe ‘yan bindigar da sojojin suka yi, amma suna shakkun bayyana farin cikinsu a fili.

Ya bukaci gwamnati da ta jibge karin jami’an tsaro domin kare sauran kauyukan da ’yan bindigar ka iya kaiwa hari.

Sai dai an yi rashin sa’ar jin ta bakin ASP Mansir Hassan, jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna wanda wakilinmu ya tuntuba a yayin tattara wannan rahoto.