✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON 2023: Najeriya ta doke Ivory Coast a wasan hamayya

Najeriya ta lallasa mai masaukin bakin yayin aragamar da aka yi a filin wasa na Alassane Ouattara.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta doke kasar Ivory Coast mai masaukin baki da ci daya mai ban haushi a Gasar Kofin Afirka ta AFCON 2023 da suka fafata a Yammacin ranar Alhamis.

A karon battar da Super Eagles ta doke Ivory Coast a filin wasa na Alassane Outtara da ke birnin Abidjan ne Najeriya ta samu nasarar farko  gasar wadda aka soma a wannan makon.

Kwallo daya ce ta raba gardamar da aka kwashe minti 90 ana yi, inda kyaftin din Super Eagles, William Troost-Ekong ya kankaro wa ’yan Najeriya martaba a bugun daga kai sai mai tsaron raga da ya jefa a minti na 54.

Wannan shan kashi da tawagar ta Ivory Coast ta yi ita ce rashin nasara ta farko aka samu wata kasa mai masaukin baki ta yi a wasannin rukuni tun bayan wadda Equatorial Guinea ta yi a shekarar 2012 lokacin da ta yi hadakar saukar baki.

Najeriya dai ta tashi daya da daya a wasanta na farko da kasar Equatorial Guinea, wanda ya sa magoya baya da dama na Najeriya suka nuna rashin jin dadinsu da sakamakon, inda wasu suke nuna yatsa ga ’yan wasan da zargin cewa ba su cika buga wa kasar kwallo da zuciya da dagiya ba kamar yadda suke yi wa kungiyoyinsu ba.

Kafin wasan dai Super Eagles na neman maki uku ne komai rintsi domin samun kwanciyar hankali, da kuma sanyaya zukatan ’yan Najeriya masu bibiyar wasannin, musamman magoya baya, da ma masu adawa.

Cote d’Ivoire dai ta yi nasara a wasanta na farko, inda a yanzu bayan wasanni biyu, ta hada maki uku, yayin da Najeriya da Equatorial Guinea ke da maki hudu-hudu, sai Guinea Bissau ita ma mai maki uku.