✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya a Aso Rock

Sarakunan sun kudiri aniyar mara wa Shugaba Tinubu baya.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawarsa ta farko da sarakunan gargajiya daga sassan kasar nan a dakin taro na Council Chambers da ke Fadar Shugaban Kasa a Abuja.

A jawabinsa na bude taron, mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar, wanda ya jagoranci takwarorinsa wajen taron, ya ce sarakunan sun ziyarci shugaban ne domin taya shi murna tare da bayyana goyon bayansu gare shi.

Ya ce majalisar sarakunan gargajiya cike ta ke da kwararru daga bangarori daban-daban na ayyukan al’umma.

Sarkin Musulmi ya ce a shirye suke su rika amsa kiransa a duk lokacin da ya bukace su

Sultan din na Sakkwato ya kuma bayyana fatan da sarakunan gargajiyar suke da shi na ganin Tinubu ya dawo kasar nan kan turbar ci gaba, inda ya ce za su mara masa baya a kan aikin da ya ke yi na saita Najeriya.

Shi ma da yake jawabi, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Adewusi, ya bukaci shugaba Tinubu da ya kara amfani da sarakunan gargajiya musamman wajen magance matsalar rashin tsaro.

A cewarsa, “mai girma shugaban kasa ka yi amfani da mu, ka yi amfani da mu, ka yi amfani da mu.”

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume; Sarkin Kano, Obi na Onitsha, Tor Tiv, Etsu Nupe, Deji na Akure.

Sauran sun hada da Shehun Borno, Elegushi na Ikate, Jaja na Opobo, Lamidon Adamawa, Sarkin Zauzzau, Gbong Gwom Jos, Attah Igala, Alake na Egbaland da wakilin Oba na Benin.