Shugaban Kasa Bola Ahmed ya gana da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Anthony Blinken a Fadar Gwamnatin Najeriya ta Aso Villa da ke Abuja.
Ana kyautata zaton tattaunawar za ta shafi hulɗar dangantaka a fannin tsaro, karfafa ɓangaren lafiya da kuma ci gaban tattalin arzikin Afirka.
- Kotu ta tsare Dan Bilki Kwamanda kan cin zarafin Kwankwaso
- An yi asarar N150m a gobarar kasuwar wayoyin salula a Yobe
Tawagar da tarbi babban jami’in na gwamnatin Amurka ta kunshi Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, Ministan Labarai, Mohammed Idris da kuma Ministan Albarkatun Kasa, Dele Alake.
A halin yanzu, Najeriya ce ƙasa ta uku da Blinken ke ziyarta a rangadi da yake yi zuwa ƙasashen yammacin Afirka da zimmar ganin ɗorewar tasirin Amurka a Afirka.
Sauran kasashen da Mista Blinken ke ziyarta sun hada da Cape Verde da Ivory Coast da kuma Angola.
Bayan ganawar ta yau, ana sa ran Mista Blinken zai kuma gana da ’yan kasuwa gobe Laraba a Jihar Legas.