✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare Dan Bilki Kwamanda kan cin zarafin Kwankwaso

Kotun ta dage zaman sauraron shari’ar zuwa ranar Litinin, 29 ga watan Janairu.

Babbar Kotun Majistare da ke Kano ta tsare fitaccen dan siyasar nan, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda kan kalaman batanci da ya yi wa tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso.

Kotun dai ta tsare dan siyasar ne dangane da cin zarafin tsohon gwamnan na Kano, wanda a bayan nan ya ce dole ne a waiwayi batun raba Masarautar Kano da takwaransa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi.

Dangane da buƙatar neman beli ce kotun ta dage zaman sauraron shari’ar zuwa ranar Litinin, 29 ga watan Janairu, inda ta ba da ajiyarsa a gidan kaso da ke Goron Dutse.

Bayanai sun ce rundunar tsaron farin kaya ta DSS ce ta gayyaci Dan Bilki Kwamanda, kafin daga bisani a gurfanar da shi gaban Kotun Majistire da ke Nomansland bisa zargin bata suna da tunzura al’umma.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa gwamnatin Kano ce ta gurfanar da shi ba hukumar DSS.

Ya ce, “ba DSS ne suka kaini kotu ba gwamnatin Jihar Kano ce ta kai ni kotu, kuma duk abin da aka yi shiryawa aka yi.

“DSS sun gayyace ni kuma na amsa gayyata, ni ne na kai kai na wurinsu sun kuma yi abin da shi ne doka.

“Abin da muke son alƙalai su dinga yi su daina aiki da umarnin wani, su yi aiki da doka domin Allah zai tambayesu kowanne hukunci da su ka yi,” In ji Danbilki Kwamanda

Ana dai tuhumarsa da ɓata wa Kwankwaso suna, kan zargin cewar ya umarci gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta rushe masarautun da tsohuwar gwamnatin jihar Kano ta ƙirkiro.