✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya dakatar da harajin tsaron intanet

Majiyar Fadar Shugaban Kasa ta ce lokacin da aka ayyana dokar Tinubu ba ya Nijeriya amma a yanzu ya ji koken ’yan ƙasar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa Babban Bankin Nijeriya CBN umarnin dakatar da fara amfani da dokar cire harajin tsaron intanet.

A bayan nan dai batun soma amfani da dokar harajin yaƙi da masu aikata laifuffuka ta yanar gizo ta haifar da mahawara mai zafi a cikin kasar.

Sai dai umarnin dakatar da dokar da shugaban ƙasar ya bayar na zuwa ne bayan matsin lamba daga ɓangarori da dama da suka haɗa da ƙungiyoyin fararen hula da na ƙwadago da kuma Majalisar Wakilai wadda ta nuna ɓacin ranta da matakin.

Jaridar Punch ta ruwaito wani na kusa da fadar shugaban kasar na bayyana umarnin da shugaban kasar ya bayar, wanda ya buƙaci sake nazari dangane da wannan dokar wadda talakawa suka soma bore a kai.

Majiyar wadda ta buƙaci a sakaya sunanta ta ce lokacin da CBN ya ba da umarnin fara amfani da dokar, shugaba Tinubu ba ya Najeriya, amma da ya dawo ya ba da umarnin dakatar da ita saboda koke-koken da suka biyo baya.

Wani jami’in fadar shugaban na daban ya kuma bayyana cewar, a shekarar 2015 majalisa ta amince da dokar a karkashin mulkin Goodluck Jonathan amma ba a aiwatar da ita ba sai yanzu.

Majalisar Wakilai ta yi fatali da dokar

A makon jiya ne Majalisar Wakilai ta yi fatali da harajin tsaron intanet da CBN ya umarci bankuna su riƙa karba daga daidaikun mutane da ke aika kuɗi ta intanet.

Majalisar ta kuma umarci CBN ya gagguta janye umarnin da ya ba wa bankuna na cirar kaso 0.5% a matsayin haraji daga kuɗaɗen da aka tura ta na’urorin zamani.

Umarnin majalisar na zuwa ne bayan koke da kakkausar suka da sabuwar dokar ta CBN ke sha daga ’yan Najeriya da kamfanoni da masana da ma ƙungiyoyi.

Tun bayan bullar sanarwar CBN a ranar Lahadin makon jiya’yan Najeriya suke kokawa da ganin bankuna sun fara cirar harajin, musamman yadda suke bayyana hakan a matsayin rashin tausaya wa halin da ake ciki na matsin rayuwa a kasar.

Sauye-sauyen harajin za su kawo mana ci gaba — Shettima 

A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya bayyana cewar duk wani haraji da wannan gwamnatin ke sanyawa, ana yi ne domin inganta rayuwar talakan kasar.

Mataimakin Shugaban Kasar ya ce sauye-sauyen harajin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke kawowa suna da nufin inganta tsarin kasar ne ta yadda duk ’yan Nijeriya za su amfana baki ɗaya.

Shettima ya faɗi hakan ne ranar Asabar yayin wani taro da kwamitin shugaban kasa ya kafa kan tsare-tsaren kuɗi da haraji ya gudanar a Otel din Transcorp Hilton da ke Abuja.

Mataimakin Shugaban Kasar ya ce sabanin yadda ake yada jita-jita, gwamnati ta kudiri niyyar “kirkirar tsarin gwamnati da zai tabbatar da cin moriyar tsarin harajin da dukkan ‘yan kasa za su amfana.”

Kashim wanda ya samu wakilcin mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan ayyuka, Dokta Aliyu Modibbo Umar, ya ce gwamnati ba ta da burin tsawwala wa ’yan Nijeriya.

“Burinmu shi ne sake farfado da tsarin haraji a Najeriya yayin da muke neman abokan hulɗa da za su sanya hannun jari mai ɗorewa kuma kasarmu ta zama wadda ake gogawa da ita da fuskar kasuwanci a duniya baki daya.”