✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya buɗe iyakokin Najeriya da Nijar

Tinubu ya bayar da umarnin cire duk wasu takunkumai da aka kakaba wa Nijar.

Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin buɗe iyakokin kan tudu da na sama da ke tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar tare da ɗage duk wasu takunkumai da aka ƙaƙaba wa kasar nan take.

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Ajuri Ngelale ya fitar a wannan Larabar.

Sanarwar ta ce wannan umarni ya dace da shawarar da Shugabannin Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) suka yanke a babban taron da suka gudanar na musamman a ranar 24 ga Fabrairun 2024 a Abuja.

Mista Ngelale ya ce shugabannin na ECOWAS wanda shugaba Tinubu ke jagoranta, sun kuma janye duk takunkuman da aka ƙaƙaba wa Jamhuriyyar Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.

Mai magana yawun shugaban kasar ya ce sanarwar ta ba da umarni kan a ɗage waɗannan takunkuman da aka ƙaƙaba wa Nijar nan take da suka hada da;

1- Rufe iyakokin sama da ƙasa tsakanin Najeriya da Nijar da kuma hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci wanda ECOWAS ta saka.

2- Dakatar da duka cinikayya tsakanin Najeriya da Nijar, da dakatar da duka ayyukan da ke tsakanin Najeriya da Nijar, daga ciki har da bai wa Nijar wutar lantarki.

3- Riƙe ƙadarorin Nijar a bankunan ƙasashen ECOWAS da dakatar da kadarorin Nijar da ke a bankunan kasuwanci.

4- Dakatar da ba Nijar duk wani tallafi na kuɗi da daina cinikayya da duk wasu cibiyoyi musamman EBID da BOAD.

5- Haramcin tafiye-tafiye ga jami’an gwamnati da iyalansu.

Haka kuma Shugaba Tinubu ya bayara da umarnin cire takunkumin tattalin arziƙi kan Jamhuriyar Guinea.