✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Birtaniya Ta Haramta wa Baƙin Likitoci Zuwa Da Iyalansu

Sabuwar matsayar ita ce, duk wanda aka ba shi gurbin aiki a Birtaniya to iya shi aka baiwa.

Hukumomin Birtaniya sun haramta wa ma’aikatan kiwon lafiya na ƙetare da ke samun aiki a can tafiya da iyalansu. 

Ofishin harkokin cikin gida na Birtaniya ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. 

Sanarwar ta ce, sabbin ka’idoji samun gurbin aiki a kasar da kuma damar zama a Birtaniya ne suka ayyana hakan. 

A cikin saƙon da aka wallafa a shafin twitter, Ofishin Harkokin Cikin Gida na Birtaniya ya tabbatar da cewa, “Daga yau, ma’aikatar kula da shige da fice ta Birtaniya ta ɗauki sabbin matakai kan takardar izinin Ma’aikatan Lafiya da ke shigowa yin aiki.

“Sabuwar matsayar ita ce, duk wanda aka ba shi gurbin aiki a Birtaniya to iya shi aka baiwa damar zama banda iyalansa.”

Yayin da yake karin bayani kan sabuwar dokar, Ofishin ya ce, ma’aikatan lafiya dubu ɗari ne suka sami aiki a Birtaniya, amma sun taho da iyalansu da suka fake da su suka sadado sun haura dubu ɗari da ashirin. 

Sanarwar ta bukaci duk wani ma’aikacin lafiya da ke da niyyar shigo da iyalansa Birtaniya ya yi rajista da Hukumar da ke da alhakin kula da masu zuwa aiki, ‘yan gudun hijira da baƙin haure. 

Hakazalika, “duk wanda ke da buƙatar shigo da wani ko gudun hijira ko aiki, ya yi rajista tare da Hukumar CQC, mai kula da ingancin ayyuka da walwala.

“Wannan wani tsari ne da zai riƙa lura da yadda ake shigowa Birtaniya.”

Bayanai sun ce a bara mutane dubu ɗari uku ne suka cancanci zuwa Birtaniya, amma a bana, ba za su kai hakan ba.

Sakataren cikin gida na Birtaniya, James Cleverly MP, ya ce: “Ma’aikatan lafiya suna ba da gudummawa mai muhimmanci ga al’ummarmu, suna kula da ‘yan uwanmu. Amma wannan ba zai zama hujjar barin al’amura sakaka ba, da a karshe zai buɗe kofar ɓarna da lalacewar al’amura.”

Ya ce, barin jama’a na tururuwar zuwa Birtaniya ba abin kirki ba ne, kuma ba abin birgewa ba ne, “mun yi wa al’ummar Birtaniya alkawarin rage adadin baƙin da ke kwararowa, kuma za su cika wannan alƙawari. 

“Shirinmu yana da faɗi, zai shafi mutane da yawa, amma shi ne adalci.  Domin wannan zai tabbatar da ingancin ma’aikatan Birtaniya tare da janyo ƙwararru daga ƙasashen duniya su zo su yi aiki, kuma su yi karatu domin kawo ci gaba ga al’ummarmu da haɓaka tattalin arziƙi.

Ministar kula da jin daɗin jama’a, Helen Whately MP, ta ce: “Bakin ƙwararrun likitoci da ma’aikata a bangaren lafiya na taka muhimmiyar rawa wurin kula da lafiyar mu. Amma gaskiya maida hankali kacokan kan amfani da baki a harkar kiwon lafiya ba abu ne mai ɗorewa ba.

A karshe ta ba da goyon bayanta ga wannan sabon tsari, da zai rage yawan baƙi a Birtaniya. 

“Wannan sabon tsarin zai karfafa guiwar likitocinmu na gida da masu taimaka musu a bangaren jinya, hakan zai sa a cike gibin da ake da shi kuma a samu karuwar kwararru yan asalin Birtaniya.”

Sakatariyar harkokin cikin gida ta ce hukumar za ta tsaftace hanyar da ’yan kasashen ƙetare ke shigowa Birtaniya yin karatu. 

Ta ce wannan zai magance yadda wasu ke zuwa kasar da zuciya biyu, hakazalika zai kare mutunci da ingancin manyan makarantun Birtaniya, da kuma tabbatar da cewa suna yi wa ‘yan asalin Birtaniya amfanin da ya dace. 

Aminiya ta ruwaito cewa, a ’yan shekarun nan, likitoci daga Najeriya na tafiya ƙasashen duniya aiki, inda suke zargin cewa ba a kula da su a matsayinsu na masu lura da lafiya yadda ya kamata.