Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA) Reshen Jihar Kano ta ce babu ruwanta da yajin aikin gama-gari da kungiyar kwadago ta fara.
Sakataren NMA reshen Jihar Kano, Ali Abdulrahman, ya ce kungiyarsu ba ta cikin kungiyar kwadago ta NLC, don haka ya nesanta NMA da yajin aikin NLC.
Ya shaida wa Aminiya cewa, mambobin kungiyar “za su ci gaba da gudanar da ayyukanmu, domin mu ba cikin NLC muke ba.
“Don haka likitoci da ma’aikatan lafiya za su ci gaba da gudanar da ayyukansu a asibitoci.
- HOTUNA: Yadda yajin aikin NLC ya tsayar da harkoki a Najeriya
- Yajin aiki ya hana zaman Shari’ar Sarautar Kano
“Likitoci da sauransu dai za su kasance a bakin aikinsu, amma mutum na iya zuwa asibiti ya tarar babu wanda zai dauko masa katinsa, saboda yana yakin aiki.
“Amma mu likitoci ba za mu yi yajin aikin ba.”
Ya kuma yi kira ga mambobin kungiyar da su yi watsi da bukatar NLC su ci gaba da aikinsu 100%
Ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da wakilinmu a Kano, a ranar Litinin da NLC da sauran kungiyoyi da ke karkashinta sun fara yajin aikin neman karin mafi karancin albashi.