Jami’an ‘yan sanda sun cika hannu da wani likitan bogi da ya buɗe asibiti yana yi wa jama’a tiyatar ƙaba (hernia) da tsakuwar ciki (appendix) a Jihar Legas.
Likitan bogin mai shekara 38 wanda bai wuce matakin karatun sakandire ba, ya buɗe asibitin shekaru biyu da suka gabata, inda ya shaida laifinsa na yin tiyata ba tare da kwarewa ba.
Ya kuma tabbabatar wa kotu cewa yana karɓar Naira 150,000 don yi wa marasa lafiya tiyatar ƙaba da kuma cire tsakuwar ciki.
Mutumin da ake zargin da ke zaman shugaban asibitin Skylink da ke Ikorodu, ya ce ya kafa asibitin a shekarar 2022.
Ya kuma bayyana cewa ya samu kwarewar aikin likitanci ne a lokacin da yake aiki a matsayin mai taimaka wa malaman jinya a wani asibiti.
- An kama masu damfara ta POS a gidan caca
- Kotu ta tura wani gidan yarin kan yi wa ’yar shekara 50 fyade
“Na kafa Asibitin Skyline ne shekaru biyu da suka wuce. Ina da ma’aikatan jinya huɗu suna taimaka min wurin gudanar da aiki.”
Da yake ba da cikakken bayani game da aika-aikar da ya ke yi, ya ce da farko tiyatar ƙaba ce kadai ya ke yi.
Daga bisani wata mata ta zo da lalurar tsakuwar ciki, bayan ya yi mata duk gwaje-gwajen da suka kamata shi ne ya feɗe ta ya cire mata.
Ya amsa cewa ba shi da ilimin likitanci, kuma takardar jami’ar da aka samu a hannun sa jabu ce.
Ya tabbatar da cewa takardar shaidar kammala karatun sakandare (SSCE) ce kawai ta gaske.
Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda (AIG) mai kula da shiyya ta biyu, Olatoye A. Durosinmi, ya bayyana cewa da farko dai wanda ake zargin ya yi ikirarin zuwa Jami’ar Obafemi Awolowo, sai dai bayan bincike an gano ƙarya yake yi.
Jami’an ’yan sandan sun gano wasu takardun bogi guda biyu da ya ce a Jami’ar Obafemi Awolowo ya samo su, da kuma wata da aka ce an samo ta ne daga Hukumar Kula da Harkokin Lafiya ta Najeriya.
Tuni dai jami’an ’yan sandan suka ɗebo kayan asibitin nasa, suka kuma saka kwado suka rufe asibitin.