✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau EFCC za ta gurfanar da Hadi Sirika kan zargin N2.7bn

Cikin waɗanda ake zargin har da diyarsa Fatima kan badaƙalar kwangilar Naira biliyan 2.7.

Yau Alhamis za a gurfanar da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika a gaban kotu, kan badakalar Naira biliyan 2.7.

Hukumar Yaki da Masu Karya Arzikin Kasa (EFCC) za ta gurfanar da Hadi Sirika tare da ’yarsa Fatimah da wasu biyu ne kan badakalar kwangilar Naira biliyan 2.7 da aka bankado a ma’aikatar sufurin jiragen sama karƙashin jagorancin Sirika.

An bukaci Sirika da ya gurfana a gaban kotu tare Fatima da Jalal Hamma da kuma Kamfanin Al-Duraq Investment Ltd, a gaban Mai Shari’a Sylvanus Oriji na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Ana tuhumar su ne da laifin yin amfani da mukamansu wajen karkatar da sama da Naira biliyan 2.7 daga ma’aikatar sufurin jiragan sama a zamanin shugabancin Hadi.

Karon farko ke nan da za a gurfanar da tsohon ministan a gaban kuliya.