Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nuna damuwarsa kan matsalar da ta haifar rashin wutar lantarki a Arewacin Najeriya.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Tinubu, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin.
- Shugabannin Arewa sun yi taro kan matsalar wutar lantarki
- Sarautar Gwandu: Kotun Daukaka Kara ta dawo da Jokolo kan kujerarsa
“Shugaba Tinubu ya jagoranci ƙoƙarin gyara lalacewar wutar da ta tsayar da harkokin tattalin arziƙi a Arewa.
“Ya kira Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu, don gyara matsalar.”
Lalacewar wutar, ya tsayar da al’amuran yau da kullum wanda hakan ya shafi harkar kasuwanci.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), ya ce ’yan ta’adda ne suka lalata layin wutar lantarki daga Shiroro zuwa Kaduna.
Shugaban ya umarci Ministan Wutar Lantarki da sauran hukumomi da su gaggauta gyara wuta a yankunan da abin ya shafa.
“Shugaba Tinubu ya damu matuƙa game da lalacewar wutar lantarki. Yana so a samar da mafita mai ɗorewa domin hana aukuwa irin wannan a nan gaba.”
Tinubu ya bayar da umarnin a samar wa injiniyoyin da ke gyaran layin wutar cikakken tsaro ta hanyar amfani da sojoji.
“Shugaban ƙasa ya yi kira ga sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma, da sauran shugabanni su haɗa kai da jami’an tsaro don kare dukiyoyin jama’a,” in ji Onanuga.