Shugaba Bola Tinubu ya karrama ’yan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya da lambar yabo ta OON.
Shugaban ya bai kowacce ’yar wasa a tawagar ta Super Falcons kyautar gida mai ɗakuna 3 a rukunin gidaje na Renewed Hope da kuɗi dala dubu 100—kwatancin naira miliyan 153.
Haka kuma, shugaban ya kuma bai wa masu horas da tawagar kyautar dala dubu 50.
A ranar Asabar ce Super Falcons ta Nijeriya ta lashe Gasar kofin ƙwallon ƙafa ta mata ta kasashen nahiyar Afirka a karo na 10, bayan samun nasara a kan mai masaukin baƙi Moroko da ci uku da biyu.