✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu na daf da korar wasu ministoci

Wani tsohon Gwamna na cikin minitocin da za a sauke su a yayin garambawul ɗin.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kammala shirye-shirye don yi tankaɗe da rairaya ga Majalisar Zartarwarsa nan ba da jimawa ba, wanda zai haɗa da naɗa sababbin ministoci da kuma ƙirƙiro sabuwar ma’aikata, kamar yadda Jaridar Aminiya ta samu labari.

Sabuwar ma’aikatar da zai ƙirƙiro ita ce ta bunkasa kiwon dabbobi, wadda a baya sashe ne a Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara.

Zai ƙirƙiro ma’aikatar ce a wani ɓangare na bunkasa kiwon shanu da dabbobi don cimma manufar shirin da aka ƙaddamar a watan Agustan bara da nufin yi wa ɓangaren kiwon dabbobi jagora, kasancewar yana samar da ɗaya bisa uku cikin kaso 21 da ɓangaren aikin gona ke bayarwa ga samar da kuɗaɗen shiga ga jama’ar kasa (GDP).

Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa, ana sa ran sabuwar ma’aikatar za ta shige gaba wajen kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa, wanda yake da mummunan illa ga wadata qasa da abinci da kuma jawo asarar dubban rayukan mutane da dabbobi da kuma dukiya.

A hasashen wata majiyar, Shugaban ya yanke shawarar ƙirƙiro sabuwar ma’aikatar ce da nufin aiwatar da burinsa na samar da wuraren kiwo a matsayin hanyar kawo ƙarshen matsalar, inda gwamnonin jihohi za su samar wa Gwamnatin Tarayya filaye domin aiwatar da shirin.

Ƙarin ministoci

Wasu majiyoyin sun shaida wa Jaridar Aminiya cewa, baya ga ƙirƙiro sabuwar ma’aikatar, garambawul ɗin zai ƙunshi naɗa ƙananan ministoci a dukkan ma’aikatu ko mafiya yawansu, waɗanda a yanzu suke da minista ɗaya ɗaya.

Idan za a iya tunawa, wasu ’yan Nijeriya sun soki Shugaban Kasar bisa abin da suka kira da ‘Majalisar Zartarwa mai tarin aiki.’

Sai dai tun a farkon gwamnati a bara, Shugaban Kasar ya tabbatar da hikimar yawan ministocin da ke da hikimar yawan ministocin da ke majalisar, wadda a farko ta ƙunshi mambobi 48, da suka haɗa da Betta Edu da aka dakatar da Simon Lalong, wanda ya ajiye muƙamin domin komawa Majalisar Dattijai.

Shugaban Kasar ya nanata cewa, “Idan ka haɗe ma’aikatu da yawa waje ɗaya saboda kana son rage kashe kuɗi, to, a nan gaba kwalliya ba za ta biya kuɗin sabulu ba.”

Haka kuma a wannan garambawul ɗin za a naɗa ministoci a ma’aikatun da suke da ƙananan ministoci, kamar Ma’aitar Kula da Nagartar Aiki da kuma Ma’aiktar Jin Kai da Magance Talauci, wadda aka dakatar da ministarta, Betta Edu tun ranar 8 ga watan Junairu.

Jaridar Aminiya ta gano cewa, ma’aikatun da ba su da qananan ministoci sun haɗa da Ma’aiktar Fasaha da Tattalin Arzikin Kirkire-Kirkire da ta Harkokin Waje da ta Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnati da ta Sadarwa da ta Kikira da Tattalin Arzikin Intanet da ta Kuɗi da ta Harkokin Ruwa da ta Ma’adanai da ta Bude-Ido da ta Sufuri da ta Masana’antu da Zuba Jari da ta Kimiyya da Fasaha da ta Ayyuka da ta Wasanni da kuma ta Harkokin Mata.

Sauran sun haɗa da Ma’aikatar Harkokin Jiragen Sama da ta Makamashi da ta Kasafin Kuɗi da Tsara Tattalin Arziki da ta Wayar da Kai da ta Shari’a da kuma ta Harkokin Neja-Delta.

Jaridar Aminiya ta samu labarin cewa, a yayin da ake dakon matakin da Shugaban Kasar zai ɗauka a kan rahoton kimanta ayyukan ministocin, wanda Mai ba shi Shawara a kan Ayyukan Ministoci, Hadiza Bala-Usman ta gabatar, ana ganin siyasa za ta shafi matakin da zai ɗauka.

Ƙoƙarin samun Hadiza Bala-Usman domin ta yi tsokaci a kan matsayin kimantawar, ya ci tura har lokacin haɗa wannan rahoto.

Sai dai a watan Afrilu ta ce, za a yi amfani da bibiyar ayyukan ministocin da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar wajen tattara bayanan ayyukansu.

Sai dai an ce bibiyar wani ɓangare ne na kimantawar, ba wai kawai ita aka yi amfani da ita ba wajen kimanta ayyukan ministocin.

Wasu za a ɗaga likkafarsu, wasu za a sauke su

Ɗaya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa, wasu ƙananan ministocin za a ɗaga likkafarsu, wasu kuma za a sauke su.

Majiyar ta ce,“Ina tabbatar maka cewa, wani tsohon Gwamna na cikin minitocin da za a sauke su a yayin garambawul ɗin.

“Akwai kuma ministocin da za a ɗaga likkafarsu.”

A yayin da aka tuntubi Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara a kan Yada Labarai, Bayo Onanuga a kan wannan batu sai ya ce, “Ba ni da masaniya w kan yi wa Majalisar Ministoci garambawul.

“Abin da kawai na sani shi ne, Shugaban Kasa na shirin yi wa ’yan kasa jawabi a yayin bikin zagayowar Ranar Dimokuraɗiyya, sannan ranar Alhamis zai wuce zuwa Legas domin bikin Babbar Sallah.”